News
Rundunar Soji Ta Lalata Wurare 12 Da Ake Tace Man Fetur Ba Bisa ƙa’ida ba
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Rundunar sojin Najeriya ta ce ta lallata wurare 12 da ake tace man fetur ba bisa ƙa’ida a yankin Naija Delta da ke kudancin ƙasar.
Cikin wata sanarwar da muƙaddashin daraktan yaɗa labaran runduna ta 6 ta sojin Najeriya da ke birnin Fatakwal, Laftanar Kanal Jonah Danjuma ya fitar ranar Lahadi, ya ce dakarun sun kuma ƙwato lita 70,000 na man fetur, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Gwamnatin Tarayya Ta Bayyana Cewa ‘Yan Najeriya Su Shirya Karin Kudin Wutar Lantarki
Sojojin sun ce a wani farmakin mako guda da suka ƙaddamar tare da haɗin gwiwar sauran jami’ar tsaro sun samu nasarar lalata ƙananan jiragen ruwa shida da ƙwato bututun mai tara da aka sace, tare da kama mutum 16 da suke zargi da hannu a jihohin yankin huɗu.
Sanarwar sojojin ta kara da cewa dakarun sun ƙaddamar da farmakin ne tun daga ranar 27 ga watan Janairu zuwa 2 ga watan Fabarirun 2025.
Yankin Naija Delta ya yi ƙaurin suna da ayyukan ɓata-gari, waɗanda ke fasa bututun man fetur tare da sace man, wani abu da masana ke bayyanawa da yi wa tattalin arziin ƙasa zagon ƙasa.
Man fetur shi ne kan gaba a hanyoyin da Najeriya ke samun kuɗaɗen da gwamnati ke samu.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
