News
Za a Ci Tarar N25,000 Ga Duk Wanda Aka Kama Yana Tofar da Yawu, Majina, Bahaya Ko Zubar Da Shara A Kano
DAGA NUSAIBA ABDULLAHI TUKUNTAWA
Majalisar Dokokin Jihar Kano ta amince da wata doka da ke tanadin ci tarar Naira dubu 25 ga duk wanda aka kama yana tofar da yawu, majina, yin bahaya ko zubar da shara a tituna, shagunan kasuwanci, karkashin gadoji da sauran wuraren taruwar jama’a a fadin jihar.
Sabuwar dokar ta biyo bayan matakin da majalisar ta dauka na samar da ingantaccen tsari don kare lafiyar jama’a da kuma kyautata tsaftar muhalli a birnin Kano.
Gwamnatin Tarayya Ta Karyata Jita-jitar Karin Farashin Wutar Lantarki
Wannan doka za ta taimaka wajen tabbatar da aiwatar da ayyukan Hukumar Kawata Birnin Kano da Kula da Wuraren Shakatawa, wadda ke da alhakin tabbatar da tsaftar birnin da kyautata rayuwar al’umma.
Gwamnatin Kano ta bukaci jama’a da su kiyaye dokokin tsaftar muhalli, domin dakile yaduwar cututtuka da kuma bunkasa kyawun birnin Kano. Hukuma za ta sanya ido don tabbatar da bin wannan doka, tare da daukar matakin hukunta duk wanda aka samu da saba wa ka’idojin da aka gindaya.
