News
‘Yan Bindiga Sun Nemi Naira Miliyan 15 a Kudin Fansar Manomi da Yaransa da Suka Sace
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Wasu Yan Bindiga sun bukaci a biyasu Naira Million 15 a matsayin kudin fansa ga wani babban manomi da ma’aikacinsa guda 1 da sukayi garkuwa dasu a garin Oba Ile ta jihar Ondo.
Jaridar People Gezette ta rawaito cewa Yan Bindigar sun sace muta ne Biyu a ranar Asabar a yayin da suke hanyarsu ta dawowa daga aikin Gona a babban titin tashin jiragen sama na Opa Ille.
Da ya’ke tabbatar da faruwar lamarin ga manaima labarai kwamandan rundunar Sojan dake Kula da Ondo , Amotekun Adetunji Adelayi ya tabbatarwa da Iyalan su cewa sojoji a shiye suke domin tabbatar da ceto mutanan.
Sai dai a gefe guda”Iyalan mutanan sun fadawa manema labarai a ranar Lahadi masu garkuwar sun bukaci a basu Naira Million 15 ta wayar Talho a matsayin kudin fansa.
-
News2 days ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
Opinion6 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News2 days ago
Zaben 2027: INEC Ta Amince Da Atiku Abubakar, ‘Yan Takarar ADC 470
