Connect with us

News

Zan Iya Rantsuwa Da Al’Kur’ani  Aisha Binani Ce Ta Lashe Zaben Adamawa Ba Fintiri Ba — Kwamishinan Zabe Hudu Ari 

Published

on

1739117619739

DAGA KABIR BASIRU FULATAN

 

 

Tsohon Kwamishinan  Hukumar Zabe da ya ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben Gwamnatin Adamawa , Barista Hudu Ari ya ce bazai  taba yin nadama  ko Kuma karyata sakamako akan cewar ba ita bace ta lashe zaben a zaben shekarar 2023 ba.

Hudu ya ce tabbas bazai taba janye kalamansaba wai dan  majalisar tarayya ta amince da korar sa a matsayin wanda ya bayyana gaskiya

Cikin  wani taron manema labarai da yayi a Bauchi, ya yi rantsuwa da Alkur’ani cewa yana da shaidun da za su tabbatar da cewa Aisha Binani ta kayar da gwamnati mai ci ta Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP.

Advertisement

An dai dakatar da Barista Hudu Ari ne saboda ya ayyana Binani a matsayin wadda ta ci zabe ana tsaka da kirga kuri’u.

Idan za’a iya tunawa dai barista Audu Ari shine ya fara fitar da sakamakon zaben Jihar Adamawa inda ya ayyana Aisha Binani a matsayin wacce ta lashe zaben da kiri’u masu rinjaye

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending