News
Hukumar PCACC Ta Kama Shugaban Ƙaramar Hukuma kan zargin badakalar filin N100m a Kano
DAGA MAIMUNA RABIU UMAR
Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano (PCACC) ta kama Shugaban Ƙaramar Hukumar Ƙiru, Abdullahi Mohammed, bisa zargin sayar da filin da aka tanada don gina Filin Wasa na Kafin Maiyaki.
Ana zargin cewa Mohammed ya sayar da filin ga wani kamfani mai suna Mahasum Company da kudin da ya kai Naira miliyan 100, wanda aka tura kai tsaye a asusun bankinsa.
Yadda Cacar-baka Ta Ɓarke Tsakanin Trump Da Zelensky A Fadar White House
Mai magana da yawun Ƙaramar Hukumar, Kabir Abba Kabir, ya tabbatar da kamun Mohammed, inda ya bayyana cewa an tura jimillar kuɗi har Naira miliyan 240 tsakanin watan Nuwamba 2024 zuwa Fabrairu 2025 a asusun shugaban.
Sai dai hukumar ta bayyana cewa ta karɓo dukkan kuɗaɗen gaba ɗaya, yayin da ake ci gaba da bincike.
Hukumar PCACC ta ce Mohammed na bayar da haɗin kai, yayin da bincike ke cigaba da bankaɗo cikakkun bayanai game da badakalar.
Hukumar ta jaddada ƙudurin ta na ci gaba da yaƙi da cin hanci da tabbatar da gaskiya a tafiyar da shugabanci a
jihar Kano.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
