News
Hukumar Kula da Lafiya A Matakin Farko Ta Sabunta Asibitoci 58 A Jihar Nasarawa
DAGA ZUBAIRU M. LAWAL, LAFIA
Gwamnatin Jihar Nasarawa ta fara aikin sabunta asibitoci 58 a fadin jihar ta hannun Hukumar Cigaban Kula da Lafiya ta Firamari (NAPHDA), domin inganta lafiyar al’umma.
Shugaban hukumar, Dr. Usman Saleh, ya bayyana hakan yayin wata zantawa da manema labarai a Lafia, inda ya ce wannan aiki yana da nufin samar da ingantacciyar kiwon lafiya ga kowa. Ya bayyana cewa Bankin Duniya da wasu abokan hulda ne ke tallafa wa shirin, wanda zai inganta kayayyakin aiki da gine-ginen asibitocin da aka zaba.
Dr. Saleh ya ce ana sa ran kammala aikin kafin karshen watan Yuni 2025, yana mai yabawa Gwamna Abdullahi Sule bisa jajircewarsa wajen bunkasa lafiyar jama’a.
Ya bukaci hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki, musamman manema labarai, domin wayar da kan jama’a game da muhimmancin kiwon lafiya.
Shugaban Kungiyar Manema Labarai na Jihar, Kwamared Isaac Ukpoju, ya jaddada goyon bayan su ga wannan shiri domin tabbatar da ingantaccen kulawar lafiya a jihar.
