News
Shugaba Tinubu Ya Mika Ta’aziyyar Rasuwar Shekh Dr Idris AbdulAziz

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana jimaminsa kan rasuwar fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dr Idris Abdulaziz, wanda ya rasu da safiyar ranar Juma’a yana da shekaru 68 a jihar Bauchi.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, Shugaba Tinubu ya bayyana Dr Abdulaziz a matsayin mutum mai tsayawa kan gaskiya da rikon akida, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen tarbiyyar matasa da wayar da kan al’umma.
Kotu Ta Dakatar Da Natasha Da Akpabio Yin Hira Da ‘Yan Jarida
Shugaban ya jaddada rawar gani da marigayin ya taka wajen yaki da ta’addanci, musamman a lokacin da rikicin Boko Haram ke tasowa, inda ya kasance cikin waɗanda suka fito fili suna kira da gyara da bin tafarkin gaskiya.
Shugaba Tinubu ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa marigayin, ya kuma roƙi Ubangiji ya bai wa iyalan da mabiyansa haƙuri da ƙwarin guiwa, tare da ƙarfafa su da su ci gaba da bin kyawawan ayyukan da ya gada.