Business
Matatar Dangote Ta Dakatar Da Siyarwa ‘Yan Kasuwa Man Fetur A Farashin Naira

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Matatar man fetur ta Dangote ta ce ta dakatar da sayar da man fetur da dangoginsa a farashin naira kamar yadda take siyarwa a baya.
Cikin wata sanarwar da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X ya ce ya ɗauki matakin ne “don kauce wa rashin daidaito tsakanin farashin da muke sayarwa da wanda muke sayen ɗanyen mai, wanda har yanzu a farashin dalar Amurka muke saya.
Matatar Dangote ta ƙara da cewa zuwa yau, fetur din da muke sayarwa a farashin Naira ya fi ƙimar ɗanyen man da muke saya da Naira.
Saboda haka, ya zama dole mu dauki matakin wucin-gadi na sauya irin kuɗin da muke sayar da mai da shi domin ya yi daidai da kudin da muke sayen ɗanyen mai.
Kazalika Matatar Dangote ta ce an jawo hankalinsu a kan rahotannin da ke yawo a intanet da ke ikirarin cewa za su dakatar jigilar mai saboda wata cuwa-cuwa da ke faruwa.
A ƙarshen sanarwar, matatar ta ce za ta ci gaba da samar da mai a kasuwannin Nijeriya ba tare da tasgaro ba.
Sannan ta ce da zarar ta karɓi ɗanyen mai daga NNPC a kan farashin Naira, to za ta ci gaba da sayar da fetur a farashin Naira ita ma.
TRT Africa Hausa