Connect with us

Business

CBN Ya  Sanar Da Kara Harajin Da Ake Cajar Mutane In Sun Cire Kudi Daga Na’urar ATM.

Published

on

Wasu Ɓatagari Sun Kwashe Wa Wani Dan Kasuwa Kuɗaɗe A Asusun Banki A Kano
Spread the love

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da sabon tsarin cire kuɗi ta na’urar ATM, inda za a caje masu amfani da katin ATM na banki Naira 100 kan kowace Naira 20,000 da suka cire.

A wata sanarwa da John Onojah, mukaddashin daraktan sashen dokoki da tsarin harkokin kuɗi na CBN, ya sanya wa hannu, bankin ya bayyana cewa sabon tsarin zai fara aiki daga ranar 1 ga Maris, 2025.

Advertisement

An Gurfanar Da Matasa Biyu A Kotu Bisa Zargin Satar Leda

CBN ya bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage hauhawar kuɗin gudanar da ayyukan ATM da kuma inganta ayyukan na’urar ATM ɗin.

 

Wannan sabon tsarin ya yi daidai da sashi na 10.7 na kundin “CBN Guide to Charges by Banks, Other Financial and Non-Bank Financial Institutions (2020).”

Advertisement

Sai dai, idan kwastoma ya cire kuɗi a ATM da ke harabar banki (on-site ATM), za a caje shi Naira 100 kan kowace Naira 20,000 da ya cire.

CBN ya umarci dukkan bankuna da cibiyoyin kuɗi da su tabbatar da sun aiwatar da wannan sabon tsari kafin ranar da aka sanya.

Daga nan zuwa ranar fara aiwatar da tsarin, ana sa ran bankuna za su sanar da abokan huldarsu don kauce wa rashin fahimta da rikice-rikicen da ka iya tasowa.

Advertisement

 

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *