News
An Gurfanar Da Matasa Biyu A Kotu Bisa Zargin Satar Leda

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An gurfanar da wasu matasa biyu, Habeeb Akinbolu mai shekaru 40 da Daniel Akinola mai shekaru 45 a gaban kotun majistare da ke Ota, Jihar Ogun, bisa zargin satar bandir din leda wanda kudinsa ya kai N30,000 mallakar mai gidansu.
Ana tuhumar wadanda ake zargin, waɗanda ba a bayyana adireshinsu ba, da laifuffukan hada kai da sata.
Mai gabatar da kara, Insp. E.O. Adaraloye, ya bayyana wa kotu cewa wadanda ake zargin sun aikata laifin ne a ranar 10 ga Janairu, da misalin karfe 7 na yamma, a kamfanin Mercury dake kan babbar hanyar Lagos zuwa Abeokuta, Ota.
Adaraloye ya ce waɗanda ake zargin, wadanda ke aiki a kamfanin Mercury Mill, an kama su ne a wurin tsaro na ƙofar shiga kamfanin dauke da fakitin Ledar.
An dage sauraron karar zuwa ranar 4 ga Maris, domin ci gaba da shari’ar.
