News
Na ji Rahotan Yadda Nuhu Ribaɗo Ke San Kamani Idan Na Dawo Nageriya – El Rufa’i
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhajii Nasir El rufa’i ya yi zargin cewa ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) na shirin kama shi saboda ya yi kalamai da bai yi wa gwamnatin Tinubu daɗi ba.
El-Rufai, dai ya yi wannan zargin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Talata.
El-Rufai ya ce ” Akwai wani shiri daga ofishin ‘Nuhu Ribaɗu’ a kama ni bayan dawo wata daga tafiya, a cusa ni cikin kurkukun da ake tsare da Emefiele.
“Ina jin irin wadannan jita-jita na kamani, a tsareni da azabtarda ni a wani kurkukun dake ofishin NSA (inda aka yi zargin an azabtar da Emefiele ya yi murabus a matsayin gwamnan CBN) tun watan Yulin 2024, tun lokacin da abin da ake kira rahoton Majalisar Kaduna ya fara yawo,” in ji El-Rufai.
Daga nan sai ya ce ” Kowa ya kwantar da hankalinsa, har masu so su kama ni, ina nan dawowa zuwa 20 ga watan Fabrairu. Zan dawo domin halartar wajen bikin kaddamar da wani littafi kan tsohon shugaban kasa Ibrahim Babangida.
