News
Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranakun Komawa Makarantu

Gwamnatin Jihar Kano ta ayyana Lahadi, 6 ga Afrilu, 2025, a matsayin ranar komawar ɗalibai makarantu domin fara zangon karatu na uku na shekarar 2024/2025. Wannan sanarwa ta shafi dukkanin makarantun kwana na gwamnati da na masu zaman kansu.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na Ma’aikatar Ilimi, Balarabe Abdullahi Kiru, ya fitar, an bukaci iyaye da su tabbatar da cewa ‘ya’yansu sun koma makaranta a kan lokaci. Sanarwar ta kuma gargaɗi cewa ɗaliban da suka gaza komawa a rana da aka kayyade za su fuskanci hukunci.
Hakeem Baba-Ahmed Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa A Gwamnatin Shugaba Tinubu
Kwamishinan Ma’aikatar Ilimi, Dakta Ali Haruna Makoda, ya jaddada cewa gwamnati na ci gaba da ƙoƙari wajen inganta ilimi da samar da yanayi mai kyau domin bunƙasa nasarar ɗalibai.
Sanarwar ta kuma bayyana fatan alheri ga malamai da ɗalibai yayin da ake shirin fara zangon karatu, tare da tabbatar da cewa za a sanya ido sosai domin ganin cewa malamai da sauran ma’aikata na gudanar da ayyukansu yadda ya dace.
