News
Kotu Ta Dakatar Da Natasha Da Akpabio Yin Hira Da ‘Yan Jarida
Babban Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarni ga Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, Shugaban Majalisar Dattijai Godswill Akpabio da wasu, da su daina bayar da hira ko wallafa bayanai kan karar da ke gaban kotu a kafafen yada labarai da shafukan sada zumunta, har sai an kammala sauraren shari’ar.
Mai shari’a Binta Nyako, wacce ta karɓi jagorancin sauraren karar daga hannun Mai shari’a Obiora Egwuatu, ta bayyana cewa hakan na da muhimmanci domin tabbatar da adalci kan shari’ar.
An sauya alƙalin ne bayan da Egwuatu ya janye daga karar bisa zargin son kai da wasu ke masa dangane da lamarin Akpabio.
-
News2 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News1 day ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News2 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
