News
Hakeem Baba-Ahmed Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa A Gwamnatin Shugaba Tinubu
Dokta Hakeem Baba-Ahmed, wanda aka naɗa a matsayin mai ba Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shawara kan harkokin siyasa, ya aike da takardar murabus daga mukaminsa a cikin makonni biyu da suka wuce, bisa dalila na kashin kansa.
Majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun tabbatar da samun takardar murabus ɗin, duk da cewa ba a bayyanawa jama’a ko an amince da bukatar tasa ba har yanzu.
“Saudiyya Ta Bankado Gaskiya: Babu Takunkumin Visa Ga Najeriya Da Sauran Kasashe 13”
Baba-Ahmed, wanda aka naɗa a watan Satumba 2023, ya wakilci gwamnati a muhimman taruka na ƙasa da na siyasa. Sai dai a shekarar 2024 ya fuskanci suka daga Ƙaramin Ministan Harkokin Tsaro, Bello Matawalle, bayan wata takaddama da ta shafi kalamansa kan Ƙungiyar Tsofaffin Shugabannin Arewa (NEF), inda ya taɓa zama kakaki kafin shiga gwamnati.
“Ya kamata mu mai da hankali wajen kawo mafita da cigaba, ba cin zarafi da kushe ƙungiyoyin da ke da tarihi na neman cigaban yankin ba,” in ji Baba-Ahmed a lokacin da yake mayar da martani kan kalaman Matawalle.
A martaninsa, Matawalle ya bayyana cewa duk wani jami’in da Shugaba Tinubu ya naɗa na da nauyin kare da tallata ayyukan gwamnati, yana mai jaddada bukatar biyayya da haɗin kai.
Hakeem Baba-Ahmed, ɗan asalin jihar Kaduna, sananne ne a fagen siyasa da mulki, musamman saboda tsayuwarsa kan gaskiya da kishin yankin Arewa. Kafin naɗin nasa, ya kasance Daraktan Yaɗa Labarai na Ƙungiyar Dattawan Arewa, sannan kuma ya riƙe mukamin Shugaban Ma’aikata a ofishin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Bukola Saraki.
Murabus ɗinsa ya haifar da ce-ce-ku-ce, musamman a arewacin Najeriya, inda masu lura da harkokin siyasa ke bayyana hakan a matsayin wani al’amari da zai iya tasiri ga huldar yankin da gwamnatin Tinubu.
