Opinion
Muhimmin Sako Zuwa Ga Gwamnonin Jihohin Arewa, Da Manyan Arewa Baki Daya!!!
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu alaikum
Ya ku masu girma manyan mu da shugabannin mu na arewa, ya kamata ku sani, yanzu haka jihar Legas ita kadai, tayi shiri na musamman domin samar da wutar lantarki har megawatts dubu hudu (4,000mgw), kusan abinda kasar Najeriya ta ke da shi kenan, kuma har wannan shiri yayi nisa sosai. Kuma ku sani, wallahi yin hakan zai zama sanadiyyar janye masana’antu da harajin kasar baki daya zuwa birnin Legas.
Ina aiko da wannan sako ne zuwa ga re ku domin ku kara farkawa, ku fadaka, domin kuma ku fara tunanin nemo wa arewa mafita in dai har da gaske kuke yi.
Wannan sauke hakki ne da Allah Subhanahu wa Ta’ala ya dora muna mu sanar da ku. Idan kuma kun yi watsi da shi, to Allah shaida ne akan cewa mun sanar da ku.
Allah yasa mu dace, Allah ya baku ikon duba wannan sako da idon basirah, amin.
Nagode,
Wassalamu alaikum,
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. 08038289761.
Laraba, 27/11/2024.
-
News6 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News2 days ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News7 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
