Connect with us

Opinion

Tabbas Mu Muke Jefa Kawunan Mu Cikin Matsaloli —Imam Murtadha Muhammad Gusau

Published

on

Tabbas, Mu Muke Jefa Kawunan Mu Cikin Matsaloli!
Spread the love

 

Assalamu alaikum

 

Advertisement

Misali, mutum ne duk wata matsala da yake ciki da damuwar da yake ciki, yana dorata akan zaluncin Shugabannin sa, amma kuma a haka za’a bashi kudi, ko taliya, ko atamfa, ko omo, ya sake zaben wadannan Shugabannin da wakilan da yake zargin sune silar wahalar sa.

Kuma bayan sun hau mulkin yaci gaba da zagin su da dora masu laifi, amma kuma wannan bai hana in suna son su dore, suci gaba da mulki, sai su sake bashi wannan kudin da suka sata daga dukiyar sa, ya sake zaben su.

Rundunar ’Yan Sanda Ta Dakatar Da Jami’anta Da Ga Aiki Saboda Satar Sama Da Naira Miliyan 43

To don giman Allah ina tunani da lissafi anan?

Advertisement

Wallahi ba mai zabe da ake ba kudi da taliya da atamfa ba, ko delegate da za’a baiwa miliyan 10 don ya zabi mugun shugaba, ko shi baya da tunani da lissafi, domin hasarar da zai yi ta rashin shugabanci na gari, tafi wannan miliyan goma din da ya karba.

Tun da sau da yawa wani zai bayar da wannan miliyan goma, domin ya nemi takardun izinin zama kasa mai ci gaba, wadda ta samu shugabanci na kwarai, wanda shi ya sayar da tashi kasar akan miliyan goma.

Sannan mutum ne zai auri mace, ya haifi ‘ya’ya, wadanda yasan sunfi karfin samun sa, a daidai lokacin da ‘ya’yan ke cikin tsananin bukatar kulawar sa, sai ya tattara su ya tura bara ko almajirci, yace sune zasu samar wa kansu abinci, da abin sha, da sutura, da magani, da ilimi da tarbiya, kuma wai sune zasu kare kansu daga masu son sace su, ko suke son gurbata su, ko suke son cutar dasu, amma idan damana tayi zai kira su, su zo su taya shi noma, idan aka gama noman sannan ya sake tura su akan titi. A dakin da ya kamata su zauna su rayu a gidan, sai ya kara aure ya saka a ciki, kuma abincin da ya kamata suci sai ya rinka ciyar da amaryar sa da shi.

Advertisement

 

Idan kace masa bai kamata ya watsar da ‘ya’yan sa haka ba akan titi, sai yace ai karatu ya kai su suyi, kuma kai da kake magana akan hakan makiyin karatun Alkur’ani kake a wurin sa, idan kace masa ai a garin su ma akwai makarantun Alkur’ani, sai yace ai idan ba aje aka yi bara ba ba’a samun Alkur’ani. Kuma kullum yana jin masu wakiltar kasar Nigeria a Musabakar Alkur’ani ba irin wadannan masu baran ne ba. Yanzu don Allah ina tunani da lissafi anan?

Sannan, maganar haraji da ake yi, ai duk mun san a kasashen turai ana karbar haraji, har wanda ya wuce tunanin duk wani mai tunani, amma kuma ai ana yiwa mutane aiki da shi, suna gani a kasa. Amma a kasashen mu da cin hanci da rashawa da facaka da dukiyar al’ummah suka dabaibaye mu, yawan kakaba muna haraji, wallahi ba shine mafita ba. Domin ko an tattara kudaden harajin, ina rantsuwa da Allah, babu abunda talaka zai gani sai karin bakin ciki da damuwa!

Advertisement

Ya kamata fa mu gyara, sai Allah ya gyara muna. Amma matukar bamu gyara ba fa, to muyi tsammanin gyaran Allah, muna yaudarar kawunan mu ne kawai!

Allah ya sawwake, yasa mu dace, ya bamu ikon gyara, amin.

Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya.

Advertisement

 

08038289761.

 

Advertisement

Laraba, 04/12/2024.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *