Connect with us

News

APC Ta Lashe Dukkan Kujerun Shugabancin Kananan Hukumomi Da Kansiloli A Katsina

Published

on

APC 4
Spread the love

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

 

Jam’iyyar APC ta yi nasarar lashe dukkanin kujerun shugabancin kananan hukumomi 34 da kujerun kansiloli 361 a Jihar Katsina, a zaben da aka gudanar kwanan nan.

Advertisement

 

Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Katsina (KTSIEC), Lawan Faskari, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Katsina.

 

A cewarsa, jam’iyyun siyasa guda biyar ne suka yi rijistar shiga zaben, amma babu babbar jam’iyyar adawa kamar PDP da NNPP a ciki. Jam’iyyun da suka tsayar da ‘yan takararsu sun hada da BP, AAC, ADC, AD, da kuma APC mai mulki.

Advertisement

 

Faskari ya yabawa al’ummar jihar da suka fito suka kada kuri’unsu cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.

Haka nan, ya jinjinawa jam’iyyun da suka sha kaye bisa hadin kan da suka bayar, tare da bukatar su mara baya ga wadanda suka yi nasara domin ci gaban jihar baki daya.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *