News
An Tsinci Gawar Jami’in Dan Sanda A ‘Dakin Otal
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
An tsinci gawar wani Sufeton ’Yan Sanda, mai suna Haruna Mohammed, a cikin wani ɗakin otal dake Jihar Ogun.
Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Ogun, Omolola Odutola, ce ta tabbatar da faruwar lamarin bayan rahotan da shugabar hotel din takai wa hukumar yan’sanda.
Aminiya ta rawaito jami’in Dan’sanda Ya je Otal G Royal da misalin karfe 1:00 na dare da ke rukunin gidaje na Anthony Uzum tare da wata mata a ranar Asabar.
Sai dai kuma da misalin ƙarfe 8:52 na safiyar washegari ne, manajar otal ɗin, Deborah Adejobi, ta gano cewar ɗakin da suka kama ba a kulle yake ba.
A lokacin da ta shiga, sai ta tarar da ɗan sandan a kwance babu rai, kuma matar da suka zo tare ba ta cikin ɗakin.
Bayan binciken da Otal din ya yi yn gano matar ta gudu bayan ta je wajen masauƙin baƙi da misalin ƙarfe 6 na safe, inda ta nemi ruwan sha.
Rotanni sun tabbara da cewa ba’a gano Marigayin, dan sandan ba ne sai daga baya aka gano kuma yana aiki da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Ishashi ta Jihar Legas.
Tuni dai aka ɗauke gawarsa zuwa ɗakin ajiyar gawa na Life Channel Mortuary da ke Olambe .
’Yan sanda sun fara neman matar da ta tsere, kuma ana ci gaba da bincike don gano dalilin mutuwarsa.
