Connect with us

Opinion

Wani Bangare Na NNPP Ya Kori Kwankwaso Da Buba Galadima Daga Cikin Jami’yyar 

Published

on

1739032356053

DAGA KABIR BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

Jam’iyyar NNPP ƙarƙashin jagorancin Dakta Agbo Major ya tabbatar da korar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Buba Galadima da baki ɗaya tawagar ƴan Kwankwasiyya daga jami’yyar, biyo bayan taronsa na ƙasa da aka gudanar a Jihar Legas a ranar 4 ga watan Fabrairu.

Haka kuma ya tabbatar da zaɓar Dakta Agbo Major a matsayin sabon shugaban jam’iyya da kuma sababbin mambobin Kwamitinta na Ayyuka na Ƙasa (NWC).

Advertisement

A yayin ganawarsa da manema labarai a hedikwatar jam’iyyar dake Abuja, ranar Asabar, Dakta Major ya ce jam’iyyar tana ƙoƙarin bin hukuncin Babbar Kotun Jihar Abia inda ta amince da Kwamitin Amintattu ƙarƙarshin jagorancin Dakta Boniface Okechukwu Aniebonam har zuwa lokacin da za a kawo ƙarshen ɓarakar da ke cikin jam’iyyar.

Dakta Major ya kuma ce sun bi hanyoyin doka ne wajen gudanar da zaɓukan jam’iyyar, ya na mai watsi da ikirarin halascin shugabancin ƴan Kwankwasiyya.

Advertisement

Ya ƙara da cewa, taron ya yi sanadiyyar dawowa da asalin tambarin jam’iyyar tare da soke wani nau’in da ƴan ɓangaren Kwankwasiyya suka gabatar a baya.

Kazalika, ya ce nan ba da jimawa ba hukumar zaɓe, INEC, za ta sabonta jaddawalin shugabancin jam’iyyar kamar yadda kotun ta bada umarni.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending