Connect with us

News

Babban Sufeton Ƴan Sandan Najeriya Ya Janye Sammacin Da Ya Yi Wa Sarki Muhammadu Sanusi II

Published

on

images (1)

Rundunar ‘Yan Sanda ta Kasa ta soke gayyatar da ta aikewa Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, domin ya bayyana a gaban hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja.

Sanarwar da kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar a ranar Asabar ta bayyana cewa Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ne ya dauki wannan mataki, bayan shiga tsakani da tuntubar wasu manyan masu ruwa da tsaki a cikin kasa, wadanda suka bukaci a bi hanyar da za ta tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Advertisement

Gayyatar Sarkin Kano: Ya Kamata Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Tsare Mutuncinta

Duk da soke gayyatar, Sufeto Janar ya umurci rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kano da su karbi bayanin Sarkin a cikin jihar, maimakon a taso keyarsa zuwa Abuja, domin ci gaba da bin diddigin batun cikin lumana da natsuwa.

Egbetokun ya jaddada cewa wannan mataki na daga cikin kudirin rundunar na kare martabarta da tabbatar da cewa aikinta na tsaro bai rikide zuwa harkokin siyasa ba, ko kuma a fassara shi da wani salo mai cike da rudani.

Advertisement

Wannan lamari dai na ci gaba da daukar hankali a fadin kasa, musamman ganin yadda siyasar Kano ke da matukar tasiri da kuma dumbin sha’awa a zukatanal’umma.

 

Advertisement

DAILY TRUST 

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending