News
Gayyatar Sarkin Kano: Ya Kamata Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya Ta Tsare Mutuncinta
DAGA IMAM MURTADHA GUSAU
Da Sunan Allah, Mai Rahama, Mai Jinkai
Assalamu alaikum
Ya ku ‘yan Najeriya! Yau ranar Asabar, 05/04/2025 mu ‘yan Najeriya mun tsintsi kawunan mu a cikin wani abun al’ajabi, wani abun mamaki, abun ban haushi, kuma abun dariya. A inda muka ji cewa wai rundunar ‘yan sandan Najeriya sun gayyaci Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Dr. Muhammad Sanusi II, domin wai yaje Abuja, ya amsa wasu tambayoyi. Ba domin komai ba, kawai sai don Mai Martaba Sarki ya tafi yayi gaisuwar Sallah ga mahaifiyarsa mai babban daki (Allah ya kara mata lafiya da nisan kwana), da kuma mai girma gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Wanda a yayin wannan ziyarar gaisuwar ne, makiya jihar Kano, wadanda basu kaunar jihar Kano, wadanda basu so su ga jihar Kano taci gaba, wadanda suke so su ga sun kunna wutar rikici da tashin hankali a jihar, suka tura yaron su, ya nemi ya tayar da hankali, amma Allah ya kare, duk da cewa wani bawan Allah ya rasa ransa a wannan lamari.
Madalla Da Ganduje Gwarzon Zaman Lafiya, Mai Kishin Ƙasa Da Kishin Kano.
Kamar yadda kowa ya sani ne, da ma sunyi haka ne da gangan, saboda su tsorata Mai Martaba, su tsorata al’ummar jihar Kano baki daya. To amma sun manta da cewa, Mai Martaba Sarki ba matsoraci bane. Sun manta da cewa, al’ummar jihar Kano ba matsorata bane.
Maimakon su tsorata, sai ga shi a lokacin da Mai Martaba Sarki zai tafi ziyarar gaisuwa ga mahaifiyarsa da mai girma Gwamna, mutum sama da miliyan biyu suka raka Mai Martaba Sarki a wannan ziyara, domin su nuna wa duniya cewa suna son Sarkin su, kuma suna tare da shi.
To wannan lamari fa ya kara tayar da hankalin makiyan jihar Kano. Sun rude, sun rikice, sun dimauce, domin har suna cewa wai ba mutane kawai ne suka raka Sarki ba, wai har da aljannu. Shine a halin yanzu suka biyo ta yin amfani da jami’an ‘yan sanda, domin suci gaba da wannan yaki da kowa yasan ba komai bane, wallahi siyasa ce.
To anan, muna kira ga rundunar ‘yan sandan Najeriya, da su dubi Allah, suji tsoron Allah, kar su bari mutuncin su ya zube a idon Kanawa, da ‘yan arewa, da ‘yan Najeriya baki daya.
Ya kamata rundunar ‘yan sanda su sani, su fa ba ‘yan siyasa bane. Su jama’ah ne na kowa da kowa. Babban aikin su shine, su kare rayuka da dukiyoyi da mutuncin dukkanin ‘yan Najeriya, ba tare da nuna banbancin kabila, ko addini, ko yare, ko bangare ko kuma jam’iyyah ba. Kuma ya kamata su sani, wallahi idan har suka ci gaba da bari wasu ‘yan siyasa suna amfani da su, domin cimma wani buri nasu na siyasa, to da zarar ‘yan Najeriya suka fahimci hakan, to za’a samu matsala, domin za’a wayi gari talakawa basu sake ganin girman ‘yan sanda kuma.
Domin jiye masu wannan tsoro, shi yasa muke kira ga rundunar ‘yan sandan kasar mu mai albarka Najeriya, da suyi taka-tsan-tsan, su kama girman su da mutuncinsu.
Sannan ya kamata mu tunatar da rundunar ‘yan sandan Najeriya cewa, masarautun mu fa suna da mutunci da daraja da Martaba a idon mu. Kuma taba su tabbas, hakika, ko shakka babu, kamar taba mu ne.
Kuma sannan me yasa ne irin wannan bita-da-kulli ba’a yinsa a kudancin kasar nan, sai a arewa kadai?
Sannan duk duniya ta sani, kuma ta shaida, kuma ta tabbatar da cewa, Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Dr. Muhammad Sanusi II an cire shi ne ba bisa ka’ida ba, an cire shi ne bisa zalunci. Wallahi, wallahi, wallahi Kanawa suna son Sarkin su, amma aka yi masu ba daidai ba. Yanzu wata Gwamnatin tazo, ta gyara waccan barna da wancan kuskure da aka tabka. Ta dawo wa da Kanawa farin cikinsu. Ta dawo masu da Sarkin su, ta dawo masu da abunda suke so kuma suke kauna, kamar yadda tayi masu alkawari.
A dokar kasar mu mai albarka, Najeriya, kowa ya sani, Gwamnan jiha shine yake da wuka-da-nama akan sha’anin cire Sarki a jiharsa da kuma nada shi. Shi yasa a lokacin da waccan Gwamnati tayi abunda tayi, Sarki Muhammad Sanusi II ya mayar da lamarinsa ga Allah. To amma su yanzu sun ce basu yarda ba, zasu ja da abunda Allah yayi.
Shi yasa a wurin cimma burin su na 2027, duk sun makance, basu ji, basu gani. Babu tsoron Allah ko imani a tare da su. Kuma domin cimma wannan buri nasu na siyasar 2027, wallahi basu ki ace jihar Kano ta kama da wuta ba. Basu ki ace arewa ta kama da wuta ba.
Amma da ikon Allah, da yardar Allah, Allah ba zai taba bari su cimma wannan mummunan buri nasu ba.
Kuma alhamdulillah, muna godiya ga Allah Subhanahu wa Ta’ala da yasa duk duniya ta fahimce su, kuma kowa ya gane su, kuma Kanawa sun fahimci inda wadannan mutane suka sa gaba.
Daga karshe, wannan nasiha ce ta tsakani da Allah, zuwa ga rundunar ‘yan sandan kasar mu mai albarka, Najeriya. Cewa suyi taka-tsan-tsan, su bi a hankali, domin mune muke shiga cikin al’ummah, wallahi muna jin irin maganganun da ake yi game da su.
Game da wannan lamari na jihar Kano, al’ummar Najeriya suna fadar maganganu marasa dadi game da ku. Mutane suna ganin cewa kun bari wasu ‘yan siyasa suna amfani da ku. Jama’ah suna cewa zaku bari a zubar maku da kima da mutunci.
Don haka, tsakanin mu da Allah, muna kira a gare ku, da ku kiyaye girman ku da mutuncinku.
Ya kamata kuyi aikin ku tsakani da Allah, ta yadda har ‘yan Najeriya zasu gamsu, su ji cewa kuna aiki ne domin dukkanin ‘yan kasa, ba kuna bari wasu suna juya ku bane.
Tabbas, hakika, wannan gayyata da kuka yiwa Mai Martaba Sarkin Kano Khalifah Dr. Muhammad Sanusi II, sam bata yi ba, kuma a gaskiya kunyi kuskure, don haka ku janye ta, domin ku tsira da girman ku da kuma mutuncin ku.
Al’ummar Najeriya baki daya suna ta yin Allah waddai da wannan gayyata. Ran ‘yan kasa ya baci matuka akan wannan gayyata da kuka yiwa Sarki Muhammad Sanusi II. Kuma wannan, ina fada maku ne tsakanina da Allah!!!
Kuma ya kamata rundunar ‘yan sandan kasar mu mai albarka su sani, wallahi dukkanin ‘yan arewa, sun hadu akan cewa wannan gayyata da aka yiwa Sarki, cìn mutuncin ne da cin fuska da bita-da-kulli ga ilahirin al’ummar arewa baki daya, ba jihar Kano ko Kanawa kawai ba.
Sannan eh mun sani, a doka, ‘yan sanda suna da damar gayyatar kowane dan Najeriya idan har ana tuhumar shi da wani laifin da ake ganin ya aikata, amma kuma akwai bukatar ayi abun cikin adalci da mutunci. Kar a yarda a tuhumi mutum da laifin da kowa yasan bai aikata ba, kai hasali ma shi aka cutar!
Wassalamu alaikum wa rahmatullah wa bara ka tuh
Allah yasa mu dace, yayi maku jagora wurin bin gaskiya, da goyon bayan gaskiya komai dacin ta, amin.
Dan uwanku, Imam Murtadha Muhammad Gusau, ya rubuto daga Okene, Jihar Kogi, Najeriya. Za’a iya samunsa a lambar waya kamar haka: 08038289761.
