News
Shugaba Tinubu Ya Bayar Umarnin A Kamo Maharan Da Suka Kashe Mutane Fiye Da 50 A Filato.
Shugaban kasa Bola Tinubu ya alƙawarta kama mutanen da suka kai hari wasu garuruwa a Plateau domin su fuskanci hukunci mai tsanani ƙarƙahsin doka.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Shugaban Ƙasar Bayo Onanuga ya fitar, Shugaba Tinubu ya aike da saƙon ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka mutu a harin, bayan da wasu ƴan bindiga suka ƙaddamar da munanan hare-hare a garuruwan Ruwi da Tadai da ƙauyukan Manguna da Dafo a ƙaramar hukumar Bokkos.
Gwamnatin Tarayya Na Shirin Dakatar Da Shigo Da Na’urorin Sola Zuwa Najeriya.
Shugaba Tinubu ya jajanta wa gwamnan jihar, Caleb Mutfwang tare da kiran al’umomin garuruwan su bai wa jami’an tsaron haɗin kai wajen kama waɗanda suka kai harin domin kare garuruwansu.
Shugaban ƙasar ya kuma tabbatar wa gwamnan goyon bayansa wajen kawo ƙarshen zubar da jini da ake yi a jihar.
Sanarwar ta kuma ce shugaban ya buƙaci hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa NEMA ta yi aiki da sauran hukumomi wajen tallafa wa mutanen da ke buƙatar taimakon gaggawa sakamakon hare-haren.
“Rahoton samun hare-haren ƴanbindiga a Plateau ya matuƙar baƙanta min rai. Ba za mu lamunci hare-hare kan mutanen da ba su ji ba su gani ba. Don haka na umarci jami’an tsaro su farauto maharan, kuma dole za su fuskanci hukunci mai tsanani idan aka kama su”, in ji Shugaba Tinubu.
