Connect with us

News

Mun Rufe Dakunan Kwanan Dalibai Saboda kin bin ƙa’idojinmu ‎ ‎ ‎—MAAUN

Published

on

FB IMG 1747143642210
Spread the love

Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University da ke Najeriya (MAAUN), Farfesa (Dr.) Mohammad Israr, ya bayyana cewa jami’ar ta rufe wasu dakunan kwanan dalibai mallakar masu zaman kansu saboda rashin bin ƙa’idojin jami’ar.

A ranar Litinin da ta gabata ne jami’ar ta rufe ɗakin kwanan Al-Ansar Indabo da ke unguwar Hotoro a Kano, inda ta bayyana cewa masu gidan sun gaza bin dokokin da jami’ar ta shimfiɗa, musamman waɗanda suka shafi walwalar ɗalibai.

Kungiyar VOGPA Ta Bukaci A Dakatar Da Shagulgulan Kauyawa A Kano 

Farfesa Israr ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda ya ce jami’ar ta ɗauki matakin ne bayan da masu gidajen da abin ya shafa suka kasa amsa tambayoyi da aka tura musu duk da alwashin da suka ɗauka na gyara.

Advertisement

“Duk da muka aika musu da tambayoyi da fata na gyara, sun gaza bin ƙa’idojinmu. Wannan ya bar mu da zabi guda daya – daukar mataki domin kare ɗalibanmu da martabar jami’a,” in ji shi.

Ya ce rashin bin doka ya janyo matsaloli da dama a cikin dakunan kwanan, kamar ƙarancin ruwa da wutar lantarki da kuma yawaitar ayyukan da ke barazana ga lafiya da tarbiyyar ɗalibai.

Farfesan ya ce jami’ar MAAUN ba za ta lamunci duk wani abu da zai zubar da mutuncin da ta gina cikin shekaru 13 ba, inda ya jaddada cewa suna sahun gaba wajen tabbatar da tsaftar ɗabi’a da walwalar ɗalibanta.

Advertisement

Ya ƙara da cewa dakunan da aka rufe na zaman mallakar ‘yan kasuwa ne da jami’ar ta amince da su karkashin wata yarjejeniya ta musamman domin ɗaukar ɗalibanta.

“Wannan wani ɓangare ne na hangen nesa na mai kafa jami’ar wajen bada gudunmawa ga tattalin arziƙin jihar. Irin wadannan matsaloli ba sa faruwa a dakunan da jami’a ke kula da su kai tsaye,” in ji Farfesa Israr.

Sanarwar ta umarci dukkan ɗaliban da abin ya shafa da su fice daga dakunan bayan kammala jarrabawar zangon farko.

Advertisement

Haka kuma, jami’ar na aiki tare da hukumomin tsaro domin tabbatar da bin wannan umarni kamar yadda ya kamata.

A makon da ya gabata ma, jami’ar ta bayar da umarnin rufe ɗakin kwanan Insktaf sakamakon zarge-zargen ayyukan laifi da suka haɗa da azabtarwa, duka da raunata ɗalibai – lamarin da ya sanya jami’ar daukar mataki domin kare lafiyar ɗalibanta.

A halin yanzu, Jami’ar MAAUN da ta fara karatu a hukumance tun shekarar 2021, ba ta da nata dakunan kwana kai tsaye, sai dai ta amince da wasu gidaje masu zaman kansu domin ɗaukar ɗalibanta karkashin kulawa ta musamman.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *