News
Kungiyar VOGPA Ta Bukaci A Dakatar Da Shagulgulan Kauyawa A Kano
Kungiyar Muryar Jama’ar Karamar Hukumar Gwale, wato Voice of Gwale LG People’s Association (VOGPA), ta yi kira ga hukumomin tsaro da na al’adu da su dakatar da sabon salo na shagulgulan da ya fara yaduwa a yankin, wanda kungiyar ta bayyana a matsayin barazana ga tarbiyyar ’yan mata.
Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da sakatarenta, Comrade Waleeth Adam Bako, ya fitar a ranar Talata, inda ta ce ana gudanar da wani biki da ake kira “Kauyawa” wanda ke gudana da dare, kuma cike da abubuwan da ke sanya ’yan mata fadawa halayen da ba su dace ba.
“Kowa ya sani cewa shagulgulan Kauyawa suna kara jefa ’ya’yanmu mata cikin duhun rayuwa. Wannan abu na iya lalata duk tarbiyyar da iyaye ke kokarin ba su,” in ji sanarwar.
Kungiyar ta bukaci shugaban karamar hukumar Gwale, Hon. Abubakar Mu’azu Mojo, da ya dauki mataki cikin gaggawa domin kare al’adun yankin da kuma ceton matasa daga fadawa tarkon miyagun dabi’u.
A karshe, kungiyar ta roki ubangaji ya ba jihar Kano zaman lafiya da kwanciyar hankali.
-
News3 days ago
Wani Matashi Mai Shekaru 18 Ya Rasa Ransa Bayan Fadawa Cikin Ruwa A Kano
-
News2 days ago
Kaduna, Nasarawa, Zamfara Da Wasu Jihohi 10 Na Fuskantar Barazanar Ambaliyar Ruwa —NiMet
-
News3 days ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
