Connect with us

News

‘Yan Bindiga Sun Sace Sarki Mai Daraja Ta Ɗaya A Gaban Masu Gadi

Published

on

AFGHANISTAN UNREST TALIBAN

Wasu ’yan bindiga sun sace Sarki Obalohun na Okoloke, Oba James Dada Ogunyanda, a karamar hukumar Yagba ta Yamma, Jihar Kogi.

An sace sarkin ne da sanyin safiyar Alhamis a fadarsa da ke garin Okoloke, da misalin karfe biyu na dare.

Majalisa Wakilai Ta Buƙaci A Samar Cibiyar Rubuta JAMB A Kowace Ƙaramar Hukuma

Shaidun gani da ido sun ce ’yan bindigar sun zo dauke da muggan makamai, inda suka kai farmaki fadar, suka doke masu gadi sannan suka yi awon gaba da sarkin.

Rahotanni sun ce har yanzu ba a san inda aka kai sarkin ba.

Rundunar ’yan sanda ta jihar Kogi ta tabbatar da faruwar lamarin.

Kakakin rundunar, SP William Ovye Aya, ya ce jami’ansu tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro da ’yan banga sun fara bincike da kokarin ceto sarkin.

Advertisement

Shugaban karamar hukumar Yagba ta Yamma, Hon. Tosin Olokun, ya yi tir da harin, yana mai kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa.

A baya-bayan nan, sace-sacen mutane sun yawaita a yankin, lamarin da ke tayar da hankali ga al’umma.

 

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending