Connect with us

News

Aminu Dantata Ya Bar Mana Wasiyyar Inda Za A Binne Shi – Iyalansa 

Published

on

20250628 090027 750x375
marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantat

Daya daga cikin iyalan marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata ya bayyana cewa marigayin ya bar umarni tun kafin rasuwarsa cewa a binne shi a birnin Madina, kusa da kabarin matarsa, marigayiya Hajiya Rabi Tajo Dantata.

Hajiya Amina Umar Fulani, wacce ita ce ‘yar uwa ga uwar gidan marigayin, ta shaida hakan a hirarta da wakilin Kadaura24 na TST Hausa a safiyar Asabar.

Advertisement

An Gurfanar da Matashi Bisa Zargin Yunkurin Kashe Kansa A Kan Allon Talla A Kano 

A cewar Hajiya Amina, marigayi Aminu Dantata ya bayyana wannan bukata tasa tun bayan rasuwar matarsa a birnin Madina shekaru biyu da suka gabata.

“Ya yi wasiyya tun bayan rasuwar matarsa cewa idan shi ma Allah Ya karbi rayuwarsa, a binne shi a Madina kusa da ita,” in ji ta.

Advertisement

Tun da safiyar Asabar, shugaban majalisar malamai ta jihar Kano, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sanar da cewa za a gudanar da sallar Ga’ib ga marigayi Alhaji Aminu Dantata a masallacin Juma’a na Aliyu Bin Abi Dalib da ke Dangi a Kano, da misalin karfe 2:00 na rana.

Rahotanni sun bayyana cewa marigayin ya rasu a birnin Dubai, kuma daga can ne za a dauki gawarsa zuwa Madina domin cika burinsa na yin hutun karshe a birnin Annabi Muhammad (SAW).

Advertisement

Marigayi Alhaji Aminu Dantata ya rasu yana da shekaru 93, bayan barin tarihi mai dimbin daraja a fannin kasuwanci, sadaka da kuma alheri ga al’umma baki daya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending