Connect with us

News

Arewa Maso Gabas: Shiyyar Da Ke Da Kishin Sauyi A Cikin APC

Published

on

IMG 20250628 WA0025

DAGA MARYAM KAMSAF

Arewa maso Gabas ta sake nuna kwarewarta da kishinta na siyasa a matakin kasa, ta hanyar ɗaukar sabon mataki mai cike da hangen nesa wajen kokarin kawo sauyi a shugabancin jam’iyyar APC na kasa.

Advertisement

Yankin da ke da tarihin taka rawa a tafiyar da mulkin dimokuradiyya a Najeriya, ya kara tabbatar da cewa ba zai kasance mai zaman kallo ba a muhimman sauye-sauye da ke gudana a jam’iyyar da ke mulki.

Arewa Maso Gabas Na Neman Sauya Shugaban APC Na Kasa, Ta Ce Lokaci Ya Yi Na Sauyi

Yayin da ake ci gaba da ganin karuwar bukatu daga mambobin jam’iyyar a fadin kasa, Arewa maso Gabas ta tsaya tsayin daka wajen fitar da ra’ayinta cikin natsuwa da fahimta, tare da nuna cewa lokaci ya yi na sake nazarin tsarin jagoranci domin ciyar da jam’iyya gaba.

Advertisement

 

Wannan mataki na Arewa maso Gabas na zuwa ne a daidai lokacin da ake bukatar sabbin dabaru da tsare-tsare na inganta tafiyar da jam’iyyar, musamman ganin yadda ake kokarin sake farfado da hadin kai da karfafa jam’iyya a tsakanin shiyyoyi.

Advertisement

A cikin wannan kokari, Arewa maso Gabas ta kasance abin koyi wajen yadda ta ke tafiyar da lamarin cikin hikima da fahimta, ba tare da tada jijiyar wuya ko hayaniya ba. Hakan ya janyo yabo daga mambobi da dama na jam’iyyar a matakai daban-daban.

Baya ga haka, Arewa maso Gabas ta ci gaba da nuna goyon bayanta ga ci gaba da zaman lafiya da dorewar dimokuradiyya a kasa, tare da fatan ganin cewa duk wani sauyi da za a yi, zai zama mai amfani ga kowa da kowa a cikin jam’iyyar APC.

Advertisement

Yayin da sauran shiyyoyi ke kallon wannan mataki a matsayin wani sabon salo na siyasa mai cike da basira, Arewa maso Gabas na fatan ganin cewa kokarinta zai zama ginshiki na sabuwar tafiya mai cike da nasara a cikin jam’iyyar APC.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending