Connect with us

News

Kano Ta Yi Babban Rashi: Alhaji Aminu Alhassan Dantata Ya Rasu

Published

on

20250628 090027 750x375

Fitaccen hamshakin ɗan kasuwa kuma dattijon al’umma, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya rasu a ranar Asabar, 28 ga Yuni, 2025.

Marigayin wanda ya shahara a fagen kasuwanci, harkokin jin ƙai da tallafawa jama’a, ya rasu yana da shekaru masu yawan gaske, bayan dogon lokaci yana hidima ga ci gaban al’umma da ƙasar baki ɗaya.

An Gurfanar da Matashi Bisa Zargin Yunkurin Kashe Kansa A Kan Allon Talla A Kano 

Wani babban jigo a cikin ƙungiyoyin matasa a jihar Kano, kuma Shugaban Kano Youth Network Coalition, Comrade Dahiru Muhammad Maihula, ya bayyana rasuwar a matsayin babban gibi da ba zai cika ba a tarihin kasuwanci da jin ƙai a Najeriya.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Comrade Maihula ya ce: “Marigayi Alhaji Aminu Dantata mutum ne da rayuwarsa ta kasance misali na tsantsar nagarta, hangen nesa da sadaukarwa wajen ci gaban al’umma. Ya zamo ginshiƙi a harkokin kasuwanci da kyautatawa marasa galihu. Wannan rashi tamkar rashi ne na dukan Najeriya.”

Ya ci gaba da cewa, “Marigayin ya taka rawar gani wajen gina rayuwar dubban mutane, musamman matasa da masu ƙaramin ƙarfi. Ya kafa tarihi wanda zai ci gaba da kasancewa abin koyi ga ƙarni-ƙarni masu zuwa.”

Jaridar INDA RANKA ta tattaro cewa, Alhaji Aminu Dantata na daga cikin fitattun ’yan kasuwa da suka taimaka wajen gina Kano a matsayin cibiyar kasuwanci da hada-hadar arziki tun shekaru aru-aru da suka gabata.

Advertisement

Ya kasance mutum mai halin ƙwarai da jajircewa wajen tallafawa al’umma ta fannoni daban-daban, ciki har da ilimi, lafiya, da harkokin taimakon gaggawa.

A halin yanzu, ana ci gaba da fatan Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa, ya sa Aljannar Firdausi ta zamo makomarsa, tare da baiwa iyalansa da dukan al’ummar Kano haƙurin jure wannan babban rashi.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending