News
Sama Da Fursunoni 7,500 Gwamnati Ta Saki Domin Rage Cunkoso A Gidajen Yari
A kokarinta na magance matsalar cunkoso a gidajen gyaran hali na kasar nan, Gwamnatin Tarayya tare da hadin gwiwar jihohi da kungiyoyin agaji masu zaman kansu, sun saki fursunoni 7,646 daga watan Janairu na shekarar 2022 zuwa Yuni 2025.
Punch ta ruwaito cewa, an saki fursunonin ne ta hanyoyi daban-daban, ciki har da bayar da afuwa, tallafin kungiyoyin agaji da kuma hukuncin da manyan alkalai suka yanke domin rage yawan masu laifi a gidajen yari.
Kididdiga ta nuna cewa a shekarar 2022 an saki fursunoni 707, yayin da 4,678 suka samu ‘yanci a 2023, sai kuma 1,843 a 2024. A farkon rabin shekarar 2025 kuwa, adadin ya kai 418.
Mafi yawan wadanda suka samu ‘yancin sun hada da wadanda suka kasa biyan tarar da kotu ta ci su, inda gwamnati da kungiyoyi suka samar da tallafin da ya kai sama da naira miliyan 585 domin biyan tarar su, a karkashin shirin alhakin zamantakewa.
Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya bayyana cewa wannan mataki na rage cunkoso ya taimaka wajen rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen kula da fursunoni, inda ya ce a baya ana kashe sama da naira biliyan daya wajen ciyar da su.
Sai dai duk da wannan kokari, matsalar cunkoso a gidajen yari na Najeriya na ci gaba da zama babban kalubale ga tsarin gyaran hali.
Rahoton Hukumar Gyaran Hali ta Kasa ya bayyana cewa a halin yanzu akwai fursunoni 81,746 a duk fadin kasar, duk da cewa gidajen yari da ake da su an gina su ne domin daukar mutum 50,000 kacal.
Daga cikin wadannan fursunoni, mutane 54,013 na jiran shari’a ne, inda da dama daga cikinsu ke fuskantar tuhumar laifuka masu nauyi kamar fashi da makami, kisan kai da sauran laifuka masu tsanani.
Gwamnati dai na ci gaba da kokarin inganta tsarin gyaran hali ta hanyar gina sababbin cibiyoyi guda biyu a jihohin Ribas da Abuja, wadanda za su iya daukar fursunoni 6,000 kowannensu idan an kammala.
