News
Fursunoni Sama Da 8,000 Sun Samu Tabin Hankali Sakamakon Yanayin Da Ake Tsare Da Su A Najeriya.
Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS) ta ce tana da fursunoni 8,246 da ke fama da matsalolin tabin hankali a gidajen yari na ƙasar.
Wannan bayani ya fito ne a lokacin zaman sauraron jama’a na uku na kwamitin bincike mai zaman kansa kan zargin cin hanci, amfani da iko ba bisa ka’ida ba, da azabtarwa a hukumar, wanda aka gudanar a Abuja.
Gwamnatin Gombe Zata Kirkiri Sabbin Kananan Hukumomi Guda 13
Mataimakiyar Kwamptrolan Janar mai kula da kiwon lafiya, Dr Glory Essien, ta ce yanayin tsare mutum a gidan yari kan iya jawo masa matsalar kwakwalwa tun daga lokacin da aka kulle shi.
“Da zarar mutum ya shiga gidan gyara hali, ya rasa ‘yancinsa, hakan kan iya tayar masa da wata matsala ta kwakwalwa. Wasu ma nan take suke nuna alamun tabin hankali,” in ji ta.
Ta ce hukumar na amfani da shugabannin fursunoni da aka horar don gano waɗanda ke nuna alamun tabin hankali, su kuma sanar da jami’an lafiya.
“Idan ka samu fursunoni 500 zuwa 1,000 kana da likita guda ɗaya, ba zai yiwu a kula da kowa yadda ya kamata ba,” in ji ta.
Dr Essien ta kara da cewa rashin magunguna, ƙarancin ma’aikata da matsalar sufuri na daga cikin ƙalubalen da suke fuskanta.
A nasa bangaren, Mataimakiyar Kwamptrolan Janar mai kula da bangaren magunguna, Mohammed Bashir, ya ce gwamnati tana iya bakin ƙoƙarinta wajen samar da kayan kiwon lafiya, amma kuɗin da ake samu bai wadatar ba.
Ya ce daga cikin fursunoni 81,122 da ke gidajen yari 256 a Najeriya, kusan kashi 2.3% mata ne. Ya ƙara da cewa sayen kayan tsabta ga mata masu haila na cin sama da naira miliyan huɗu a wata
