Connect with us

News

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba —RAHOTO

Published

on

Kotu ta yanke wa Muhammad Buba hukuncin daurin rai da rai bisa laifin kashe mahaifinsa

Biyo bayan rahoton baya-bayan nan da ya bayyana cewa fursunoni sama da 86,000 ke tsare a gidajen yarin Nijeriya, inda kashi 70 cikin 100 daga cikinsu ba a yanke musu hukunci ba, kamfanin hada-hadar kudi na Moneda ya kaddamar da gidauniya domin ceto fursunonin da ke tsare ba tare da hukunci ba.

Babban jami’in gudanarwa na kamfanin, Ejike Egbuagu, ne ya kaddamar da Gidauniyar Egbuagu a wani biki da aka gudanar a hedkwatar kamfanin da ke Lekki, Jihar Legas. Wannan taron ya zo daidai da cikar Egbuagu shekaru 40 da haihuwa, kuma ya samu halartar manyan lauyoyi da kwararru daga fannin shari’a.

Advertisement

‎Sheikh Indabawa Ya Bukaci Al’umma Da Su Kare Kansu Kafin Su Shiga Jimamin Jinkirin Jami’an Tsaro. ‎

“Gidauniyar Egbuagu za ta mayar da hankali ne wajen ‘yantar da fursunonin da ake tsare da su ba bisa ka’ida ba, musamman matasa masu basira,” in ji Egbuagu yayin jawabin kaddamarwar.

Gidajen Yari Sun Cika Fiye Da Kima

Advertisement

Rahoton Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta kasa ya nuna cewa, har zuwa 28 ga Afrilu, 2025, an samu cunkoso da kima a gidajen yari da ke aiki da kashi 136.7 cikin 100 na yawan fursunonin da ya kamata su dauka. Wannan na nuna irin halin rashin walwala da rashin adalci da yawancin fursunonin ke fuskanta.

A cewar kididdiga, kimanin yara 26,000 na zaune a gidajen yari, wasu daga cikinsu an haife su ne a can, wasu kuma ana tsare da su ba tare da cikakken bayani ko tabbacin aikata laifi ba.

Advertisement

 

Gidauniyar Za Ta Fara Da Fursunoni 1,000

Advertisement

 

Egbuagu ya bayyana cewa gidauniyar za ta fara ne da yunkurin ‘yantar da fursunoni 1,000 da aka tsare ba bisa ka’ida ba. Ya ce an riga an fara tuntuba da tsara yarjejeniyoyi da hukumomin da abin ya shafa, da kuma kamfanonin lauyoyi da za su bayar da gudunmuwa – wasu a matsayin aikin sa-kai, wasu kuma za a biya su idan bukatar hakan ta taso.

Advertisement

“Mafi yawan wadannan fursunoni ba su da ma fayil ko takardun da ke bayyana laifin da ake zarginsu da shi. Za mu samar musu da fayil-fayil, tare da duba dalilan da yasa bai kamata su ci gaba da zama a kurkuku ba,” in ji shi.

Lauyoyi Da Masana Sun Bayar Da Goyon Baya

Advertisement

Daya daga cikin manyan lauyoyin da suka halarci taron, Zikora Okwor-Wewan, ta bayyana jin dadinta da wannan tsari, tana mai cewa:

“Na dade ina aiki da fursunonin da ke jiran shari’a da kuma wadanda aka tsare ba bisa ka’ida ba. Wannan gidauniya za ta taka muhimmiyar rawa, kuma na kuduri aniyar bayar da gudunmuwa ta musamman.”

Advertisement

Egbuagu ya bayyana cewa cikakken aiwatar da wannan aiki zai fara nan da watan Yuni, 2025, kuma an tsara a kammala matakin farko cikin kwanaki 90.

Shirye-shirye Na Musamman

Advertisement

Gidauniyar za ta mayar da hankali kan matasa fursunoni masu basirar kirkire-kirkire, inda za a tallafa musu su amfani da kwarewarsu, har ma daga cikin gidan yari. Bincike zai mayar da hankali kan shekarunsu da irin laifin da ake zarginsu da shi, domin tantance cancantar sakin su.

Kididdiga Mai Takaici

Advertisement

A cewar Egbuagu, daga cikin kimanin fursunoni 80,000 da ke gidajen yari a Najeriya, kusan 70 cikin 100 na ci gaba da dakon hukunci. Haka kuma akwai matsaloli da dama da suka hada da rashin shaidar haihuwa, rashin takardun shari’a da kuma tsarin da ke hana samun saukin sauraren karar su cikin lokaci.

 

Advertisement

 

LEADSHIP

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending