Connect with us

News

Kwamishina Waiya Ya Yi Wa Gwamna Abba, Kwankwaso, Gwarzo Da Al’ummar Musulmi Barka Da Sallah

Published

on

KANOShiga Zanga Zanga Ba Zai Kawo Karshen Tsadar Rayuwar Da Ake Cike Ba Kwamitin Zaman Lafiya
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya,

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf da al’ummar Musulmi murnar zagayowar bikin Babbar Sallah.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Kwamishinan ya ce wannan lokaci na Sallah dama ce ta godiya ga Allah da kuma tunawa da darussa na biyayya, hadaya da sadaukarwa.

Kashi 70 Na Fursunonin Nijeriya Ba A Yanke Musu Hukunci Ba —RAHOTO

“Ina mika sakon fatan alheri ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a wannan lokaci mai albarka. Allah Ya kara masa nasara da jagoranci nagari,” in ji shi.

Haka kuma, ya mika gaisuwar Sallah ga Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, yana mai fatan Allah Ya kara masa lafiya da kwanciyar hankali.

Kwamishina Waiya ya kuma taya Jagoran Kwankwasiyya na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso (PhD), da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sunusi II, murnar zagayowar bikin cikin koshin lafiya.

Ya ce ya na kuma taya Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano, Isma’il Falgore, da ‘yan majalisar jiha da ta tarayya, da mambobin Majalisar Zartarwa ta jihar murnar Babbar Sallah.

Advertisement

“Ina mika fatan alheri ga daukacin al’ummar Kano da Musulmi gaba daya. Allah Ya sa wannan lokaci ya zama na haɗin kai da ƙarfafa zumunci,” in ji shi.

Kwamishinan ya bukaci jama’a da su gudanar da bukukuwan cikin lumana da natsuwa, tare da yin addu’ar samun zaman lafiya da ci gaba a Jihar Kano da kasa baki ɗaya.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending