News
Kotun Canada Ta Ayyana Jam’iyyun PDP Da APC A Matsayin Ƙungiyoyin Ta’addanci
Kotun tarayya da ke ƙasar Canada ta ayyana manyan jam’iyyun siyasa a Najeriya na PDP da APC a matsayin ƙungiyoyin ta’addanci, biyo bayan rahotonta da ya tabbatar da cewa dukannin su sun taka rawa wajen kisan mutane yayin, lokacin da kuma bayan zaɓe da suna rikicin zaɓe.
Yayin da take haramta baiwa guda daga cikin ƴan siyasar Najeriya Douglas Egharevba mafakar siyasa, kotun ta ce ba zata amince da baiwa mamban ƙungiyar ta’addanci mafaka a ƙasar ba.
Fursunoni Sama Da 8,000 Sun Samu Tabin Hankali Sakamakon Yanayin Da Ake Tsare Da Su A Najeriya.
A wani hukunci da ya yanke tun ranar 17 ga watan Yulin da ya gabata mai shari’a Phuong Ngo ta ce ba za’a iya baiwa ɗan siyasar mafaka ba, kasancewar bai cika ƙa’idojin da hukumar kula da shige da fice ta ƙasar na tabbatar da tsaro ba.
Kafafen yaɗa labarai na duniya sun ruwaito cewa ministan kula da tsaro da harkokin cikin gida na ƙasar ya ce jam’iyyun suna kashe mutane kai tsaye da sunan rikicin kafin, yayin da kuma bayan zaɓe, don haka ki tsaye wannan ta’addanci ne.
Douglas Egharevba mamba ne jam’iyyar PDP ne a tsakanin shekarun 1990-2007, kafin daga bisani ya koma jam’iyyar APC.
To sai dai da suke mayar da martani jam’iyyun PDP da APC sun musanta batun alaƙarsu da ƴan ta’adda.
Da take musanta alaƙarta da duk wani ta’addanci, jam’iyyar PDP ta ce kotun bata da wata hujja da ta dogara da ita wajen yanke wannan ɗanyen hukunci.
Itama a nata ɓangare jam’iyya mai mulki ta APC ta ce wannan hukunci ne da kai tsaye ke taɓa mutuncin Najeriya, kuma abu ne mai matuƙar haɗari.
Ƙarƙashin wannan hukunci dai Canada ba zata bar duk wani mamban jam’iyyun nan guda biyu ya shiga ƙasarta ba.
