News
Rikici Kan Ruwa Ya Yi Sanadin Mutuwar Matashi A Kano
Wani matashi dan shekaru 17, Musa Muhammad, ya mutu bayan wata arangama da abokinsa a Rijiyar Lemo da ke cikin birnin Kano.
Lamarin ya faru ne a safiyar Asabar, lokacin da Musa ya fita dibar ruwa daga wani famfo a unguwar, kamar yadda kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar.
A cewar sanarwar da rundunar ta fitar, mahaifin mamacin, Muhammad Haruna, ya kai rahoto ofishin ‘yan sanda na Bachirawa, inda ya bayyana cewa rikicin ya faro ne akan gardama tsakanin Musa da abokinsa, Muhammad Aliyu, mai shekaru 16.
“Gardamar ta rikide zuwa fada, inda ake zargin Muhammad Aliyu ya bugi Musa a fuska. Sakamakon hakan, Musa ya fadi ya sume,” inji sanarwar ‘yan sanda.
An garzaya da Musa zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.
Bayan haka, an mika gawar mamacin ga iyalansa domin gudanar da jana’iza bisa tsarin addinin Musulunci.
Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa an kama wanda ake zargi, kuma ana ci gaba da bincike kan lamarin.
SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zarar an kammala bincike.
