News
Ƴan Bindiga Sun Yi Ajalin Manoma 27 A Wani Sabon Hari A Filato
Aƙalla mutum 27 ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai a safiyar Litinin a ƙaramar hukumar Riyom da ke Jihar Filato, lamarin da ke ƙara ƙarfafa damuwar al’umma kan tabarbarewar tsaro a yankin tsakiyar Najeriya.
Shugaban ƙungiyar matasan Birom ta BYM, Dalyop Solomon, ya tabbatar da faruwar harin ga manema labarai, inda ya bayyana cewa maharan sun kutsa garin ne da misalin ƙarfe 5:30 na asuba, inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi tare da cinna wuta a gidajen mazauna yankin.
Jam’iyyar PDP Ta Musanta Tsayar da Ɗan Takarar Gwamna a Nasarawa
“Yanzu haka mun tabbatar da mutane 27 da suka mutu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su asibiti. Za a sanar da ranar jana’izar su nan gaba,” in ji Solomon.
Harin ya auku ne a daidai lokacin da lamarin rashin tsaro ke ƙara ta’azzara a wasu sassan jihar Filato, inda ake ta fuskantar hare-hare tsakanin manoma da makiyaya da kuma farmaki daga wasu gungun ’yan bindiga da ba a tantance ko su wane ba.
A martanin ta, ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah reshen Jihar Filato ta nesanta kanta daga harin, tana mai bayyana cewa ba su da hannu ko kaɗan a wannan ta’addanci.
Shugaban ƙungiyar, Ibrahim Babayo, ya ce: “Wannan hari ba mu da alaka da shi. Zargin da ake yi mana babu wata hujja da za ta goya masa baya.”
Sai dai har zuwa lokacin da aka fitar da wannan rahoto, gwamnatin jihar Filato ba ta fitar da wata sanarwa ko martani a hukumance dangane da harin ba.
