Connect with us

News

Ƴan Sanda Sun Gano Bama-Bamai Da Makamai a Cikin Kayan Bola a Kaduna

Published

on

images (1)

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kaduna ta gano wasu bama-bamai na soja da ba su fashe ba tare da tarin makamai da aka boye a cikin wani kayan bola da aka kawo daga jihar Borno.

‎Wannan ya haifar da damuwa kan yadda ake jigilar kayan daga yankunan da ke fama da rikici.

Advertisement

Tsofaffin Kansilolin APC Sun Barranta Kansu da Kalaman Abdullahi Abbas, Sun Bayyana Goyon Bayan Su ga Gwamna Abba

‎A cewar sanarwar da jami’in hulda da jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, an gano abubuwan ne a ranar 2 ga Agusta, 2025, bayan samun bayanan sirri daga majiya mai tushe.

‎An gano bama-baman a wani kamfanin tattara shara da ke Kudandan, a karamar hukumar Kaduna South.

Advertisement

‎Kungiyar kwararru daga sashen tarwatsa bama-bamai (EOD) karkashin jagorancin kwamandan ta isa wurin nan da nan, inda suka tabbatar da cewa kayan da aka gano bama-bamai ne da ba su fashe ba.

‎An kwashe su zuwa wuri mai aminci domin tarwatsa su bisa ka’idojin tsaro.

Advertisement

‎Bincike ya kuma gano wasu makamai da suka hada da bindigar hannu da aka kera a gida dauke da harsasai shida da harsasai 18.

Advertisement

‎An rufe kamfanin don ci gaba da bincike da tabbatar da babu sauran kayan fashewa.

‎Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Rabiu Muhammad, ya haramta shigo da kayan bola daga yankunan dake fama da rikici, musamman daga Arewa maso Gabas.

Advertisement

‎Ya umarci dukkan DPO da Area Commanders su kama duk wanda ya karya wannan doka, tare da kira ga jama’a su rika bayar da bayanan sirri kan duk wani abu da suke zargi.

 

Advertisement

PREMIUM TIMES 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending