News
Tsofaffin Kansilolin APC Sun Barranta Kansu da Kalaman Abdullahi Abbas, Sun Bayyana Goyon Bayan Su ga Gwamna Abba
Tsoffin kansiloli da suka taba rike mukamai a karkashin jam’iyyar APC a jihar Kano, ciki har da wasu daga cikinsu da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP, sun gudanar da zanga-zanga domin nesanta kansu daga kalaman da shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, ya yi a kwanakin baya.
Shugaban kungiyar tsofaffin kansilolin, Sunusi Kata Madobi, ne ya jagoranci taron tattaki da sama da tsofaffin kansiloli 3,000 suka halarta a harabar ma’aikatar yada labarai da ayyukan cikin gida da ke sakatariyar Audu Bako.
A jawabin da ya gabatar yayin taron, Madobi ya musanta ikirarin da Abdullahi Abbas ya yi na cewa wai tsofaffin kansilolin ne suka turo domin su yi wa gwamnatin NNPP yakin sunkuru. Ya ce wannan magana ba gaskiya ba ce, kuma “shiftin gizo” ce kawai.
“Mun zo ne da zuciya daya domin nuna goyon bayanmu ga Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda ya nuna damuwa da halin da muka shiga bayan barin mulki. Gwamna Abba ya maida mu cikin mutane, don haka dole ne mu nuna godiya,” inji Madobi.
Daya daga cikin wadanda suka halarta, Hajiya Uwa Magaji daga karamar hukumar Bebeji, ta bayyana cewa su ba yaran Abdullahi Abbas ba ne.
“Maganar da yake yi cewa wai sun turo mu don mu yi wanke-gara siyasa, wannan ba gaskiya ba ce. Kyawawan halayen Gwamna Abba ne suka janyo mu, ba wani umarni daga Abdullahi Abbas ba,” inji ta.
Haka zalika, tsohon kansila daga Gezawa, Dahiru Yusuf, ya ce gwamnatin tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ta hana su hakkokinsu, don haka su na ganin gwamnatin Abba ta fi cancanta da goyon baya.
“Maganar Abdullahi Abbas kanmu karya ce. Gwamna Abba ne kadai ya nuna niyyar biyansu hakkinsu ba tare da neman wani sakamako daga gare su ba. Wannan aiki ne domin al’umma, ba siyasa ba,” inji Dahiru.
A yayin da yake karɓar bakuncin tawagar, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa ya dauki alkawarin biyan duk wani hakkin da tsohon gwamnatinsu ta kasa biya, kuma hakan ba don siyasa ba ne, sai don adalci da kishin Kano.
“Ina fata kowa zai koma gida lafiya, kuma ku sani cewa wannan gwamnati tana kishin ‘yan Kano. Ba mu bukatar komai daga gare ku sai dai addu’a da hadin kai,” cewar gwamnan.
A ƙarshe, dubban tsofaffin kansilolin da suka fito daga sassa daban-daban na jihar sun rika rera wakokin goyon baya tare da dauke da kwalaye da rubuce-rubuce na kin amincewa da kalaman shugaban APC, yayin da suka kewaya harabar sakatariyar Audu Bako zuwa ma’aikatar kananan hukumomi domin nuna mubaya’ar su ga gwamnatin NNPP a jihar Kano.
