Connect with us

News

An Kama Matar Data Ƙone Al’aurar Ƴar Shekara 5 Saboda Fitsarin Kwance A Bauchi

Published

on

Rundunar ‘yan sanda a jihar Bauchi ta kama wata matar aure mai suna Rabi Nuhu daga garin Magama Gumau a ƙaramar hukumar Toro, bisa zargin ƙone al’aurar wata yarinya ‘yar shekara biyar. Ana zargin ta aikata hakan ne saboda yawan fitsarin kwance da yarinyar ke yi.

Rahotanni sun bayyana cewa yarinyar marainiya ce, domin mahaifiyarta ta rasu kusan shekara ɗaya da ta gabata, tana zaune tare da mahaifinta, Mohammed Umar, da matarsa wacce ake zargi da cin zarafin nata.

Advertisement

Ban Taba Nadamar Aiki Karkashin Ganduje Ba – ANWAR

Wani mai fafutukar kare haƙƙin bil’adama, Kabiru Abdulkadir, ya ce sai bayan kwana biyar da faruwar lamarin ne aka gano abin da ya faru.

“Don kauce wa matsala, mahaifin yarinyar ya saya mata katifa ta daban, amma duk da haka matar tasa ta ci gaba da azabtar da ita,” in ji Kabiru.

Advertisement

An ruwaito cewa lamarin ya bayyana lokacin da yarinyar ta roƙi kawunta ya saya mata katifa, inda ta bayyana cewa mamanta ta ƙona al’aurarta saboda yawan fitsarin kwance. Wannan ne ya sa aka kai rahoton ofishin ‘yan sanda.

Ana zargin cewa matar tana amfani da yarinyar wajen huce fushinta duk lokacin da ta samu sabani da mijinta.

Advertisement

Mahaifin yarinyar, Mohammed Umar, wanda ke aiki da gidan talabijin, ya tabbatar da cewa matarsa ta kan yi ƙorafi kan yarinyar saboda fitsarin kwance, abin da ya sa ya saya mata katifa ta daban.

“A farko, da na ga ƙuna a jikinta, matata ta ce min shayi mai zafi ne ya zubo a jikinta. Na gaskata hakan, amma daga baya sai na lura da ciwon yana ƙaruwa,” in ji shi.

Advertisement

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Mohammed Wakil, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce rahoto ya iso ofishin su da misalin ƙarfe 3:00 na rana, ranar 13 ga Satumba, 2025.

Wakil ya ce yarinyar ta sami ƙonuwa a ƙasan cikinta, cinyoyinta da al’aurarta. Ya ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Sani Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin a gaggauta kama matar tare da miƙa ta sashen manyan laifuka domin gudanar da cikakken bincike.

Advertisement

“Da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da wacce ake zargin a gaban kotu,” in ji Wakil.

AMINIYA

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending