News
Cutar Zazzaɓin Lassa Ta Hallaka Mutane 166 a Jihohi 21

Hukumar Yaƙi da Cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce mutane 166 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutar zazzaɓin Lassa a faɗin ƙasar tun farkon shekarar 2025 zuwa yanzu. Wannan adadi ya fi na mutanen da suka mutu a daidai wannan lokaci a shekarar da ta gabata.
A rahoton mako na 37 da hukumar ta fitar, an ce an samu mutane 7,673 da ake zargin sun kamu da cutar, inda daga cikinsu aka tabbatar da mutum 895 da gwaji.
Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kisa Bayan Surfawa Shugaban Kasa Ashar
Rahoton ya nuna cewa cutar ta bulla a ƙananan hukumomi 106 da ke cikin jihohi 21 daga cikin jihohi 36 na ƙasar.
A cikin mako na 37 na wannan shekarar, an samu sabbin mutum 146 da ake zargin sun kamu da cutar, inda aka tabbatar da mutum 11 daga cikinsu, mutum biyu kuma suka mutu a jihohin Ondo, Bauchi, Kogi da Anambra.
Cutar zazzaɓin Lassa cuta ce mai tsanani wadda ƙwayar “Lassa virus” ke haddasawa, kuma tana yaduwa ne ta hanyar mu’amala da ɓeraye ko kuma kayan abinci da suka gurɓata da najasa ko fitsarinsu.
Hukumar NCDC ta shawarci jama’a da su kula da tsaftar muhalli da kuma guje wa mu’amala da abinci ko ruwa da suka gurɓata, tare da gaggauta zuwa asibiti idan sun lura da alamomin cutar.