Connect with us

News

Kungiyar FPA Ta Yi Allah Wadai Da Janye Jami’an Tsaro Daga Bikin Cikar Najeriya Shekaru 65 A Kano

Published

on

IMG 20251005 WA0003

Ƙungiyar Forum of Progressive Academics (FPA) ta bayyana matsananciyar damuwarta tare da yin Allah wadai da abin da ta kira “tsarin siyasa na gangan” da ya kai ga janye jami’an tsaro daga wajen bikin cikar Najeriya shekaru 65 da aka gudanar a Kano, matakin da ta ce “ba shi da wata hujja mai ma’ana”.

‎Shugaban ƙungiyar, Dr. Abubakar Isa Ibrahim, ne ya bayyana haka yayin taron manema labarai da aka gudanar a Sakatariyar yan jaridu ta NUJ a Kano, inda ya zargi wasu masu ruwa da tsaki da siyasantar da harkokin tsaro don cimma manufofinsu.

Advertisement

Jami’an ’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi Da Sace Hakimi A Kano

‎“Mun taru ne domin bayyana damuwarmu kan wannan sabon salo na amfani da harkar tsaro wajen cimma manufofin siyasa. Janyewar jami’an tsaro daga wajen bukin ba wai kawai abin mamaki ba ne, illa kuwa tsari ne na gangan don lalata shirin,” in ji Dr. Ibrahim.

‎Ƙungiyar ta bayyana takaicinta kan yadda sauran jihohin ƙasar suka gudanar da bikin cikar shekaru 65 cikin tsaro da halartar jami’an tsaro, sai dai Kano kaɗai aka ware daga hakan.

Advertisement

‎Ƙungiyar ta kuma roki Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta daukar matakin da ya dace don dawo da amincewar al’umma ga hukumomin tsaro da tabbatar da adalci a jihar.

‎Dr. Ibrahim ya yi kira ga al’ummar Kano da su tsaya tsayin daka wajen kare martabar jiharsu, sannan ya gargadi waɗanda ke da hannu a cikin wannan yunkuri cewa za su fuskanci hukunci a siyasa.

Advertisement

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending