News
An Buƙaci Kotu Ta Hana Jonathan Tsayawa Takara A 2027
Wata babbar kotun tarayya da ke zaune a Abuja, ta samu buƙatar dakatar da tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, daga tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ko kowanne zaɓen shugaban ƙasa nan gaba.
Wannan buƙata ta fito ne daga wani lauya, Johnmary Jideobi, wanda ya shigar da ƙara gaban kotun. A cikin ƙarar, mai ƙarar ya nemi a hana Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Najeriya (INEC) karɓa ko wallafa sunan Jonathan a matsayin ɗan takara.
Majalisar Wakilai Ta Kafa Kwamiti Don Duba Harkokin Kuɗin Kirifto Da POS A Najeriya
Mai ƙarar ya bayyana cewa Jonathan ya kammala wa’adin mulki biyu da Kundin Tsarin Mulki ya tanadar: na farko bayan wafatin marigayi shugaban ƙasa Umaru Musa Yar’Adua, sannan na biyu bayan nasarar da ya samu a zaɓen 2011.
Duk da buƙatar da aka shigar, kotun ba ta sanya ranar fara sauraron ƙarar batukuna.
