Connect with us

Politics

Sanata Barau : An Faro Daga Mazaba An Yadu A Ko’ina

Published

on

Barau
Spread the love

DAGA ABBA ANWAR 

Ina ga makaho ne kadai ko wani mai son zuciya ne zai ce ba ya ganin hobbasar da wannan bawan Allah yake yi kan cigaban al’umma da kuma yin aikinsa yadda kundin tsarin mulki ya ayyana.

Tabbas aikin duk kowane dan majalisa na ainihi ya faro ne kuma ya takaitu kan yin dokoki tare da ‘yan uwansa ‘yan majalisa. Amman duk da haka fa shi wannan mara kwarafniyar ya yarda da yin wasu abubuwan da alhakin yin su ya rataya ne kan bangaren masu zartasawa a gwamnati.

Kada ki binciki wayar mijinki ba tare da izinsa ba – Gargadin Shehu Sani

Idan za a yi nazari da kyau za a fahimci cewar shi fa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Kasa, wanda kuma shine Mataimaki Na Farko a Majalisar Cigaban Kasashen Afirka ta Yamma, wato ECOWAS Parliament, Sanata Barau I. Jibrin, ya kawo tsafta da rashin kwarafniya a siyasar mazabarsa wato Kano ta Arewa. Sannan kuma amfanin wakilcinsa a na jin sa a matakin kasa da ma na wannan nahiya tamu ta Afirka.

Advertisement

Yadda zancen kuma yake shine, yin tituna da gina ajujuwan makarantu ko sharar gonaki da sauransu, ba shine ainihin aikin dan majalisa ba a doka. Amma fa duk da haka wannan Sanatan ya dauki ire-iren wadannan abubuwan ya sa su cikin tsare – tsarensa na hidimtawa al’umma.

Mai karatu zai iya tuna jami’ar gwamnatin tarayya ta kimiyya da fasaha ta Kabo (Federal University of Science and Technology, Kabo), wacce wannan Sanata mai kishin jama’arsa ya mika kudurin kafa ta, tare da bin sawun ganin kudurin ya samu tsallake dukkan matakan yin doka. Haka ya kara bin sawun ganin kudurin daga karshe ya samu sahalewar Shugaban Kasa.

Haka kuwa a ka yi. Da kan sa wannan Sanata ya yi gine-gine a muhallin da a ka samawa makarantar. Har Allah Ya sa ta mike ta fara aiki ka’in da na’in.

Kamar kuma yadda tsarin gwamnati yake a ko’ina, cewar ita fa gwamnati aba ce kamar mai rai. Tsare tsaren mulki ba sa taba tsayawa. To irin haka su ma ayyukan majalisa suke. Idan ka kalli irin hobbasar da Barau ya yi wajen ganin aikin titin Gwarzo na gwamnatin tarayya ya ci gaba, za ka san mutum ne shi sahihi.

Advertisement

Bayan nan kuma a can baya kafin ma ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, shine sila na samar da harabobin nesa (satellite campuses) na jami’ar National Open University of Nigeria (NOUN) a dukkanin kananan hukumomin da suke a mazabarsa ta Kano ta Arewa. Bayan nan kuma ya yi hobbasar samar da gine-ginen da wadannan harabobi za su iya amfani da su.

Wato yadda ya ba ilimi kulawa ta musamman, hakan ne ya sa ya zama ya yi fice tsakankanin ‘yan uwansa ‘yan majalisa, yaransu da mayansu. Ka ga kuwa yabanya ta samu yaduwa a matakin kasa.

Shi kullum babban burinsa shine gina dan Adam. Wannan ne ya sa bai tsayar da ma’auninsa ga mazabarsa kawai ba. Shi ba dan siyasar da ya kulle kansa iyakacin mazabarsa ba ne. Wato “local politician.” Ya na amfani da kaifin basira da gogewa wajen zabawa kansa irin ayyukan da ya kamata ya yi na taimakawa al’umma.

Rashin kwarafniya da kuma ganin girman kowa ya sa ya yi fice tsakanin tsararrakinsa na majalisa da ma sauran ‘yan siyasa. Hakan sai ya samu taimako daga Allah na kariya daga kulle-kulle da kisisina da kuma ingiza mai kantu ruwa. Shi din sai Allah Ya hore masa dabarun sanin me yake so, da fahimtar abinda yake so din. Kuma ta yaya yake son cimma wannan abun. Abubuwan sa cikin nutsuwa da hankali da rashin kwarafniya mara kan gado.

Advertisement

Ba tare da fargabar cakuda zance da rikirkita zance ba, zan iya cewa, Sanata Barau wata Aya ce daga Allah Madaukakin Sarki. Wanda Allah Yake kare shi daga kulle – kulle-kullen magabta na gaske da kuma wadanda ke yi bisa rashin fahimtar yadda abin yake.

Bayan fa yadda ya sha wuya na ba-gaira-ba-dalili haka kawai ba tare da laifin komai ba, a can baya, sai Allah Ya kawo masa wani dauki kuma na musamman. Har a halin da a ke ciki yanzu, ya na daga cikin ‘yan siyasar da a ke ganin girmansu a kasar nan. Ka ga shi yaduwar tasirinsa ya wuce iyakacin mazabarsa kadai. Ya kai matakin kasa. Kai har ma ya tsallaka ga matakin wannan nahiya tamu ta Afirka ta Yamma.

Shi fa wannan bawan Allan idan ka dauki dubunnan daliban da yake daukar nauyin karatunsu a jami’o’in ciki da wajen Najeriya, za ka fahimci cewar kwarewarsa ta sa ya san yanayin zamantakewar al’ummar kasar nan. Saboda samar da yanayin cigaban kasa. Ba musu a kan hakan. Shi ba dan siyasa ne da kansa yake a kulle iya mazaba ba.

Wani abinda kuma yake daure min kai shine, yadda wasu ke tunanin cewa wai Sanata Barau ya yi watsi da yadda yake taimakawa jama’a a baya. A rashin fahimta da son zuciya na irin wadannan mutane har yanzu idonsu bai nuna musu dalibai dubu daya (1,000) da suka fito daga Kano ta Arewa, wadanda kwanan nan a ka yi bikin daukar nauyin karatunsu da Sanata ya yi ba a Jami’ar Bayero dake Kano (Bayero University, Kano).

Advertisement

Haka nan duka a kwanan nan, ko sati biyu ba a yi ba, da a ka kara yin wani bikin na daukar nauyin dalibai dubu daya (1,000) daga mazabarsa a Jami’ar Ilimi ta Gwamnatin Tarayya ta Yusuf Maitama Sule, a Kano (Yusuf Maitama Sule Federal University of Education, Kano).

Hakan zai ci gaba da yi a ragowar manyan makarantun jihar Kano. Yayin da za a yi bikin daukar nauyin karatun daliban da su ka fito daga mazabarsa.

Sai nake mamakin irin maganganun da wasu ke yi cewar wai Sanata Barau ya yi watsi da ayyukan alherin da yake yi a baya. Amma duk mai hankali zai gane cewa, wannan maganar son zuciya ce kawai. Ba dadi ba ragi. Kar mai karatu ya manta fa, har yanzu ina yi wa Barau kallon wata Aya daga Allah Mai Kun-Fa-Yakun!

Idan ba a manta ba kuma fa a satin da ya wuce ne ya rarraba tallafi ga jama’a na kudi sama da Naira Miliyan Dari Biyu. Ban san ko da me ire-iren wadanda ke yin suka mara dalili za su ce kan wannan kokarin ba kuma. Sai ya kasance kamar ga haske a na nunawa mutum amma yana rintse ido.

Advertisement

Daga fa lokacin da Sanata Barau ya samu shiga majalisar dattawa zuwa yanzu din nan da a ke magana, idan a ka tattara irin kudaden da ya kashe, kan abubuwan alherin da yake wa al’umma ba kawai na mazabarsa ba, daga daukar nauyin karatu da gina ajujuwan makarantun sakandare da na firamare da tallafin al’umma da daukar nauyin maganin marasa lafiya da karfafa kasuwancin jama’arsa da sauran muhimman abubuwan rayuwa, za ka iske ya kashe Bilyoyin Nairori ne.

Amincewarsa da samar da yanayin walwala ga al’umma ta sa ya yi irin tasa hobbasar wajen samar da hasken wutar lantarki a kauyuka da daman gaske.

Kuma babban abin alfaharin ma shine yadda ‘yan uwansa ‘yan majalisa su ka amince da ingancinsa da nagartarsa da jajircewarsa. Hakan shi ya sa suka dinga ba shi shugabancin kwamitoci masu matukar amfani ga rayuwar majalisa. Ya rike shugabancin kwamitin man fetur. Ya rike shugabancin kwamitin kula da yadda a ke rarraba arzikin kasa (Appropriation Committee). Irin kwamitin da ya taba rikewa lokacin ya na majalisar wakilai ta kasa, lokacin Kakakin Majalisar na Wakilai, marigayi Ghali Umar Na’Abba. Allah Ya jikansa da Rahama. Ya kuma rike shugabancin kwamitin Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund).

Yanzu kuma cikin taimakon Allah shine Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa na Kasa. Tafi tafi ma har ya kai ga samun Mataimakin Na Farko Na Shugaban Majalisar Raya Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS Parliament). Mai karatu ka dai ga yadda Allah Yake aikinSa.

Advertisement

Saboda fa yarda da ingancin wakilcinsa da kuma sanin yakamantansa wajen hulda da jama’a, sai da kai ta kawo kungiyar yan jaridu na majalisar kasa su ka ba shi wata gagarumar yabawa da ba su taba ba kowa ba a mafi tsahon lokaci. Wato “2024 Highest Development – Driven Bills Award.”

Samun irin sa a majalisa sai an tona da kyau. Mutum mai kawaici da rashin kwarafniya da kuma tsinkaye mai amfani.

Lokaci kadan fa kafin ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ba irin wulakanci da hada shi fada da jama’ar da ba ai ba. A ka mayar da shi saniyar ware. A ka sa masa karan tsana. Amman da yake Allah ne ke yi ba dan Adam ba, sai ga shi hakan ya zame masa hassada ga mai rabo.

Ni fa idan ta nine zan cewa jam’iyyar APC ta kasa, ya kamata a daukaka likkafar Sanata Barau zuwa can sama kusa da kololuwa ko a wannan kewayen da’irar idan zaben 2027 ya zo. Ni a waje na wannan bawan Allan a ce likkafarsa kar ta takaita iya Kano kawai a zaben 2027 mai tunkaro mu. A nawa ra’ayin na kashin kaina kenan.

Advertisement

Gaskiya ne ya faro daga matakin mazaba, amman saboda halayensa na gari da kawaicinsa da girmama al’umma da sanin yakamata, sai ya zama Allah Ya dora shi saman ‘yan siyasa da yawan gaske. Wannan kuma ko wasu sun fahimta ko ba su fahimta ba.

A kuma matakin nahiya, wato Yammacin Afirka, Sanata Barau ya na yin iya kokarinsa wajen ganin ya kara samar da dankon zumunci tsakanin kasashen dake wannan nahiya. Ba ma a nan ya tsaya ba kawai, ya na yin kokari iya kokari wajen ganin dukkan tallafin da kungiyar ECOWAS ya kamata a ce ta samu daga gwamnatin Najeriya ta na samu. Daga abinda ya shafi harkar gudanar da kungiyar zuwa ga tallafin kayan aiki.

Hakan ya sa Sanatan ya kara samun tagomashi wajen shugaba Bola Ahmed Tinubu. Sai kuma ya zama wani kwararre kan huldar kasar nan da kasashen waje. Kai ka ce shi din wani jakada (Ambassador) ne na tsakanin kasa da kasa dama tuntuni.

Wani abin ban sha’awa kuma shine dama can Sanata Barau dan siyasa ne mai akidar gaba-dai-gaba-dai, tun ma fa lokacin ya na karatun jami’a. Sannan kuma a siyasar al’umma bayan kammala karatu, sai ya kara samun gogewa kan irin wannan ra’ayi daga wajen tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kano, wato marigayi Muhammadu Abubakar Rimi. Allah Ya jikansa da Rahama.

Advertisement

Shi fa wannan bawan Allan ya yarda da mafari/tushe. Hakan ya samar masa da fantsama bangarorin kasar nan tare kuma da yin tasiri a nahiyar Afirka ta Yamma.

 

Anwar ya rubuto wannan daga Kano

Juma’a, 10 ga watan Oktoba, 2025

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *