Connect with us

News

Jihar Yobe Ta Rufe Dukkan Makarantun Kwana Sakamakon Ƙaruwar Matsalar Tsaro

Published

on

Empty classroom

Gwamnatin Jihar Yobe ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun firamare da sakandare na  kwana a fadin jihar, saboda kara tabarbarewar tsaro a wasu sassan Najeriya.

Mamman Mohammed, Daraktan Hulda da Jama’a na Gwamnan Jihar Yobe, ya ce:

Advertisement

“Gwamnatin jihar ta umarci rufe dukkan makarantun sakandare na  kwana domin tabbatar da tsaron dalibai.”

Jami’an ’Yan Sanda Sun Cafke Tiktoka Da Ta Ƙirƙiri Labarin Sace Ta Don Ƙara  Samun Mabiya

Sanarwar ta bayyana cewa wannan matakin ya biyo bayan taron tsaro da gwamnan, Mai Mala Buni, ya yi tare da shugabannin tsaro, inda aka duba hare-haren da ake kaiwa makarantun a wasu sassan kasar.

Advertisement

Yobe na cikin jihohin da suka rufe makarantu saboda tsaro. A kwanakin baya, jihohi kamar Kebbi, Plateau da Kwara sun dauki matakin rufe makarantu.

A ranar Litinin da ta gabata, ‘yan bindiga sun sace dalibai 24 a Kebbi, yayin da a Neja aka sace dalibai kusan 315 a mako guda. A lokaci guda, wasu ‘yan bindiga sun kai hari coci a Kwara, inda suka sace mutane da dama tare da kashe wasu biyu.

Advertisement

 

Channel TV

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending