News
NLC Ta Jinjinawa Gwamna Abba Kan Manufofin Tallafa Wa Ma’aikata, Ta Nemi A Ƙara Taimaka Wa Fansho
Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) reshen Jihar Kano ta yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa manufofinsa na kyautata jin daɗin ma’aikata, tare da yin kira da a ƙara tallafa wa masu karɓar fansho a jihar.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin saƙon taya murnar Babbar Sallah da shugaban riƙo na ƙungiyar, Kwamared Nura Rimin Gago, da sakataren riƙo, Kwamared Abbas Ibrahim suka sanyawa hannu.
Babbar Sallah: Farashin Kayan Miya Ya Tashi Matuka A Kano
A cikin saƙon, NLC ta taya Gwamna Abba Kabir Yusuf, mataimakinsa Alhaji Murtala Sule Garo, ma’aikata, masu fansho da al’ummar Musulmi murnar zagayowar bikin Eid-el-Kabir.
Ƙungiyar ta jinjinawa gwamnatin jihar kan yadda take bai wa walwalar ma’aikata muhimmanci, musamman amincewa da bayar da tallafin naira dubu 20 ga ma’aikatan gwamnati domin rage musu raɗaɗin matsin tattalin arziki.
NLC ta kuma bayyana fatan cewa gwamnatin jihar za ta faɗaɗa tallafin zuwa ga masu karɓar fansho domin nuna girmamawa da jinjina ga gudunmawar da suka bayar wajen gina jihar tsawon shekaru.
Ƙungiyar ƙwadagon ta bayyana Gwamna Abba Kabir Yusuf a matsayin shugaba mai kyakkyawar alaka da ma’aikata, tana mai yabawa da matakan da gwamnatinsa ke ɗauka wajen biyan bashin fansho da ya haura naira biliyan 32.
Ta kuma nuna kwarin gwiwar cewa gwamnatin za ta ci gaba da cika alƙawarin da ta ɗauka na kawar da sauran bashin fanshon da ake bin jihar.
Sai dai ƙungiyar ta buƙaci ma’aikata su mayar da martani ga irin kulawar da gwamnati ke nuna musu ta hanyar ƙara himma, ƙwarewa da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
Har ila yau, ta shawarci ma’aikatan gwamnati da su guji duk wani abu da zai iya zubar da martaba da kimar aikin gwamnati tare da tabbatar da ingantaccen aiki ga al’umma.
NLC ta kuma taya Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kano Rt. Hon. Jibrin Isma’il Falgore, ma’aikata, masu fansho da daukacin al’ummar Musulmi murnar Babbar Sallah, tana mai yi musu fatan zaman lafiya da gudanar da bikin cikin farin ciki da albarka.
