News
Ibrahim Little Ya Yi Allah-wadai Da Harin ’Yan Bindiga A Shanono Da Tsanyawa
Ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a Kano, Alhaji Ibrahim Ali Amin Little, ya yi Allah-wadai da hare-haren da ’yan bindiga suka kai a kan al’ummomi a ƙananan hukumomin Shanono da Tsanyawa a jihar Kano.
A wannan makon ne aka kai harin, wanda ya haɗa da sace mata takwas, lamarin da ya ƙara tayar da hankalin mazauna yankin.
Jami’an NDLEA Sun Cafke Miyagun Ƙwayoyi Da Darajarsu Ta Haura Sama Da Naira Biliyan 6
A cikin wata sanarwa da ya fitar, Ibrahim Little ya ce matsalar tsaro a jihar na kara ta’azzara, yana mai cewa akwai bukatar gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa da suka dace.
Ya ce, “Gwamnati na da babban nauyin kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Idan aka kasa tabbatar da tsaro, to an gaza a babban aikin gwamnati.”
Little ya ce dole hukumomin tsaro su ƙara amfani da bayanan leƙen asiri tare da aiki cikin tsari domin dakile hare-haren tun kafin su faru.
Ya kuma bukaci gwamnati ta ba wa iyalan waɗanda abin ya shafa tallafi – ciki har da goyon bayan tunani da na tattalin arziki – domin rage radadin abin da ya faru.
