Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Cafke Miyagun Ƙwayoyi Da Darajarsu Ta Haura Sama Da Naira Biliyan 6

Published

on

WhatsApp Image 2025 11 26 at 10.50.35 750x430

Jami’an Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta NDLEA a Najeriya, sun bankaɗo muggan ƙwayoyi da aka ɓoye a wasu manyan ɗakunan ajiyar kayayyaki da kuɗinsu suka haura sama da naira biliyan shida da miliyan 700 a jihar Lagos.

Wata sanarwa da daraktan sashen yaɗa labarai na hukumar, Femi Babafemi ya fitar yace, yayin samamen da jami’an Hukumar NDLEA ɗin suka gudanar, sun kuma cafke wani babban dillalin ƙwaya mai suna Onyekachi Pius tare da wasu mutum biyar.

Advertisement

Jami’an NDLEA Sun Cafke Miyagun Ƙwayoyi Da Darajarsu Ta Haura Sama Da Naira Biliyan 6

Sanarwar ta ci gaba da cewa, an samu mutanen da aka cafke ɗauke da waɗannan ƙwayoyi a tattare da su, bayan samamen da aka kai maɓoyarsu da ke wani rukunin gidajee da ke Lagos.

Daga cikin kayayyakin da aka gano a hannun su, akwai maganin Tramadol da kuma kodin, wanda ake zargin sun adana ne saboda bikin Kirismeti da ke ƙaratowa.

Advertisement

A cewar NDLEA, manyan motoci aka yi amfani da su wajen fitar da tarin waɗannan muggan ƙwayoyin daga rukunin gidaje na Festac da ke yankin Apple Junction kamar yanda FRI HAUSA ta ruwaito

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending