News
KANO :Rikicin Manoma Da Makiyaya Ya Yi Ajalin Mutum Tare Da jikkata Wasu A Rogo
Rahotanni da suke fitowa daga Karamar Hukumar Rogo an tabbatar da mutuwar wani mazaunin yankin sakamakon wani lamari da ya faru da wasu Fulani da suka zo wucewa ta Garin Yanoko dake Mazabar Fulatan, a daidai lokacin da manoma ke shirin girbe amfanin gonarsu.
Wani mazaunin yankin, Malam Sabi’u Musa Yanoko, ya shaidawa Jami’in Labarai na Karamar Hukumar Rogo, Abdu Bako Abdullahi ANIPR, cewa makiyayan sun taso ne daga Jihar Kaduna.
Shugaba Tinubu Ya Amince Da Tawagar Nijeriya Ta Haɗin Gwiwa Kan Tsaro Tsakanin Amurka Da Ƙasarsa
Ya bayyana cewa mutanen yankin, saboda fargaba, suka sanar da hukumomin tsaro da sauran jami’an da suka dace domin tabbatar da tsaro ganin cewa amfanin gonarsu basu girbe ba a yankin.
Malam Sabi’u Musa ya ce jami’an tsaro, dagacin yankin da sauran masu ruwa da tsaki sun gaggauta isa wajen, kuma sun tabbatar don makiyayan su wuce cikin kwanciyar hankali ba tare da wata matsala ba.
Sai dai bayan kammala tattaunawa, rahotanni sun nuna cewa makiyayan sun kaiwa wasu mutum biyu hari, wanda ya jefa su cikin munanan raunuka.
Daya daga cikin wadanda aka jiwa rauni, Malam Haladu Jume, ya rasu bayan an garzaya da shi asibiti domin ba shi agajin gaggawa.
Malam Sabi’u Musa yayi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da Karamar Hukumar Rogo da su kara tsaurara matakan tsaro da sa ido kan motsin makiyaya har sai manoma sun kammala girbin amfanin gonakinsu cikin tsaro.
