Connect with us

News

Ƙungiyoyin Farar Hula 262 Sun Yi Watsi Da Rahoton Daily Trust Kan “Kano — New Bandits Frontier”

Published

on

Hukumomi a Najeriya sun tsaurara matakan tsaro da kuma sa ido sosai a birnin Kano,

Kungiyar Kano Patriotic CSOs Coalition Forum (KPCF) haɗan wasu ƙungiyoyi 262 ta ce rahoton Daily Trust na ranar Talata, 2 Ga Disamba 2025 mai take “Kano — New Bandits Frontier” ya ƙunshi bayanai marasa daidaito da kuma zance mai haifar da fargaba ga al’umma.

‎A cikin sanarwar da ta fitar, KPCF ta ce rahoton ya yi wuce gona da iri wajen bayyana matsalolin tsaro, tare da tsara hoton da zai iya rage kwarin gwiwar jama’a da kuma nuna Kano kamar ta zama sabuwar mazaunir ’yan bindiga.

Advertisement

Kungiyar Bakin Bulo Network for Better Tomorrow Ta Bukaci Gwamnatin Kano Ta Sake Duba Dokar Hana Goyo

‎Ƙungiyar ta ce ko da yake an samu wasu hare-haren  yan Bindiga a kan iyakar Kano da Katsina wanda hakan baya nuna cewa jihar ta zama cibiyar ’yan bindiga.

‎KPCF ta jaddada cewa Hukumomin tsaro sun gudanar da nasarorin aiki da suka haɗa da , Kashe wasu ’yan bindiga a Shanono, Ceto Waɗanda aka yi Garkuwa da su tare da Ƙarfafa tattara bayanan sirri a yankunan kan iyaka.

Advertisement

‎Ƙungiyar ta ce birnin Kano kansa bai fuskanci hare-haren ’yan bindiga ba, lamarin da ya tabbatar da zaman lafiyar jihar.

‎Sanarwar ta karyata zancen cewa akwai rashin jituwa tsakanin gwamnatin jihar da rundunar ’yan sanda.

Advertisement

‎KPCF ta ce Hukumomin tsaro a jihar sun gudanar da tarurruka akai-akai, yayin da gwamnati ke ci gaba da bai wa jami’an kayan aiki, motocin sintiri, na’urorin sadarwa da sauran tallafi.

‎Kungiyar ta ce haɗa batun Rikicin masarautu da batun tsaro abuni  wanda zai rikita jama’a  ba tare da wani dalili ba.

Advertisement

‎Ƙungiyar ta zargi rahoton da amfani da kalmomin da za su iya haifar da fargaba, musamman kalmar “new bandits frontier” wadda ta ce bata dace da ainihin halin da ake ciki ba.

‎Ta ce irin wannan rubutu yana iya ,Tsoratar da jama’a, ‎Durƙusar da sha’awar masu zuba jari, ‎Rage kwarin gwiwar jami’an tsaro, Lalata amincewar al’umma ga hukumomi

Advertisement

‎KPCF ta ce rahoton bai ba da cikakken hoto ba saboda bai ambaci abubuwan da gwamnati ke yi ba, kamar, Ayyukan hadin gwiwar jami’an tsaro a kan iyaka, Aiwtar da dokar hana karya dokokin babura na 2013, Ƙara ma’aikatan sintiri da na sirri,  Tattaunawa tsakanin hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya, Haɗin kai da jihohin Katsina da Jigawa.

‎Ƙungiyar ta ce damƙar da al’umma suka yi wajen kama masu laifi a Kofar Ruwa na nuna cewa jama’ar Kano na da wayewa da haɗin kai wajen kula da tsaro.

Advertisement

‎KPCF ta jaddada cewa Kano ba sabuwar mattarar ’yan bindiga ba ce

‎Matsalolin da ake gani na yankunan kan iyaka ne kamar yadda ake gani a wasu jihohin Arewa

Advertisement

‎Gwamnati da jami’an tsaro na aiki tare don tabbatar da zaman lafiy

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending