News
Kungiyar Bakin Bulo Network for Better Tomorrow Ta Bukaci Gwamnatin Kano Ta Sake Duba Dokar Hana Goyo
Kungiyar Bakin Bulo Network for Better Tomorrow ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta sake duba dokar hana goyo ga masu baburan Lifan da aka fara aiwatarwa a birnin.
A cikin wata sanarwa da shugabanta, Bilal Nasidi Mu’azu, ya fitar a ranar Laraba, kungiyar ta bayyana damuwarta kan illolin da dokar ka iya haifar wa al’umma, musamman iyaye mata da masu karamin karfi.
Bilal ya ce mutane da dama na amfani da baburan su wajen kai yara makaranta da gudanar da hidindimun rayuwa, don haka takurawa irin wannan na iya jefa su cikin ƙalubale.
Sanarwar ta kuma bukaci Rundunar ’Yan Sandan Kano da ta yi la’akari da koke-koken jama’a, ganin cewa dokar za ta shafi rayuwar mutane da dama, musamman mata da masu kula da kananan yara.
Kungiyar ta yi addu’ar Allah ya sauƙaƙa wa al’ummar Kano tare da ba da mafita ga kalubalen da ke tattare da wannan mataki.
-
News6 days ago
An Tsare Kwamandan NSCDC Da Wasu Jami’an hukumar Da A Ke Zargi Da Sakaci A Mutuwar Masu Hakar Ma’adanai 37 A Neja
-
News5 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Ɗalibai 6 Daga Hannun Masu Garkuwa Da Mutane A Katsina
-
News4 days ago
NLC Za Ta Fara Fafutukar Neman Sabon Ƙarin Mafi Ƙarancin Gabanin 2027 — Ajaero
