News
Shugaba Tinubu Ya Yi Wata ganawar Sirri Da Hafsoshin Tsaro
Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wata ganawar sirri a jiya talata da hafsoshin tsaron kasar nan a Fadar Shugaban Kasa dake Aso Rock .
Taron sirri, wani bangare ne na kokarin da Gwamnatin Tarayya ke yi na kara kaimi wajen magance matsalar rashin tsaro da ke kara kamari a fadin kasar.
Gwamnatin Kano Ta Sanar Da Ranar Fara Hutun Makarantun Firamare Da Sakandare
Hafsoshin tsaron sun isa Fadar da misalin karfe biyar na yamma, inda taron ya dauki kusan sa’o’i biyu.
Da yake magana jim kadan bayan kammala taron, Babban Hafsan Tsaro Janar Olufemi Oluyede, ya ce Shugaba Tinubu ya bayar da umarni tare da neman su matsa kaimi a yaki da matsalar rashin tsaro a kasar nan.
Janar Olufemi Oluyede ya bayyana taron a matsayin mai muhinmanci kuma ya nuna cewa ana sa ran sabon umarnin Shugaban kasar zai haifar da karin nasarori a ayyukan tsaro a kasar nan.
Taron ya zo ne sa’oi kadan bayan Shugaba Tinubu ya zabi tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), a matsayin Ministan Tsaro, bayan murabus din wanda ya gabace shi, Muhammad Badaru Abubakar ranar litinin, mako guda bayan an ayyana dokar ta-baci a kan matsalar tsaro.
TRUST RADIO LIVE
-
News6 days ago
KANO: Yara 24 Da Ake Tuhuma Da Laifi Sun Amfana Da Shirin Gyaran Tarbiya Maimakon Hukuncin Kotu A Watan Yuli
-
News1 day ago
Ana Zargin Matar Aure Da Shaƙe ’Yar Kishiyarta Mai Shekara 3 Har Lahira
-
News13 hours ago
Ba Za Mu Yi Wa Kowa Rangwame Ba A Wajan Yaƙi Da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi Ba — Muhyi Magaji
